✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: INEC ta dage zabukan cike gurbi 15

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage zabukan cike gurbi guda 15 da za a gudanar a jahohi 11 a fadin Najeriya. INEC ta dage…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage zabukan cike gurbi guda 15 da za a gudanar a jahohi 11 a fadin Najeriya.

INEC ta dage zabukan daga ranar Asabar 31 ga Oktoba ne bayan bullar tashe-tashen hankula sakamakon zanga-zangar #EndSARS da ta shafi yankunan da za a yi zabukan.

Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamatin Wayar da kai kan zabuka, Festus Okoye, ya ce rashin samun nutsuwa da yanayin da ake ciki na rashin tsaro da kuma rahotannin da hukumar ta samu sun tilasta mata sauya tunanin gudanar da zabukan saboda tashe-tashen hankula a sassan kasar.

Ragowar zabukan da suka rage na cike gurbi za su gudana ne a mazabun ‘Yan Majalisar Dattijai guda 6 da mazabun ‘yan majalisar jihohi guda 11.

Hukumar INEC a shirye take ta gudanar da sahihan zabukan cike gurbi a cikin makonni masu zuwa, wanda hakan na daga cikin kudurin hukumar ga ‘yan Nijeriya.

A zamanta da Kwamishinonin Zabe na jihohi a ranar Alhamis, INEC ta ce ta dage zabukan cike gurbin ne a karkashin dokar da aka sabunta wadda take kunshe cikin kundin doka ta 26 (2) na dokar zabe ta 2010.

Dokar ta ce matukar akwai alamun rashin zaman lafiya to hukumar na da damar dage zabe.