✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa da Birtaniya sun cimma matsaya a takaddamarsu kan kamun kifi

Ko a makon da ya gabata sai da Faransa ta cafke wani masuncin Birtaniya.

Shugabannin kasashen Faransa da na Birtaniya sun tattauna kan batun ikon kamun kifi a kan iyakokinsu, sakamakon ficewar Birtaniyan daga Kungiyar Tarayyar Turai (EU).

Hakan dai wani muhimmin mataki ne wajen kauce wa wata takaddamar tattalin arziki da za ta iya shafar ilahirin nahiyar Turai.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson dai sun hadu ranar Lahadi inda suka tattauna na tsawon mintuna 25 a gefen taron kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya wato G20, wanda yake gudana a birnin Rome na kasar Italiya.

Tattaunawar dai na zuwa ne kwana daya bayan Boris Johnson ya yi korafi ga Shugaban EU, Ursula von der Leyen cewa matakan da Faransa ke dauka za su iya kai wa ga samun ramuwar gayya, inda ya ce ba ta da wata hujjar aikata hakan.

Shugabannin dai sun amince su yi duk mai yiwuwa wajen magance batutuwan da suke takaddama a kansu, nan ba da jimawa ba.

Boris Johnson dai ya sha nanatawa a taron na G20 cewa dole ne dukkan masu ruwa da tsaki su yi duba na tsanaki kan babbar barazanar sauyin yanayi ga duniya, a daidai lokacin da kasarsa take shirye-shiryen karbar bakuncin sama da kasashe 120 a taron sauyin yanayi karo na 26, wato COP26 daga ranar Litinin mai zuwa.

Dukkan kasashen biyu dai na kokarin kare kansu kan matakan da suke dauka, inda ko a makon da ya gabata sai da Faransa ta cafke wani masuncin Birtaniya da take zargi da kamun kifi ba bisa ka’ida ba a wani tafkinta.

Faransa dai ta fusata ne kan yadda ta ce Birtaniya da wasu kasashe ba su ba kwalekwalen kasarta izinin kama kifi a kasashensu ba, tun bayan fara aiki da yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai (Brexit) a farkon 2021.