✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa ta haramta shan giya a bainar jama’a

Gwamnati ta sa a hukunta wasu mutane da suka shirya casun shan giya a birnin Paris

Kasar Faransa za ta haramta shan giya a bainar jama’a a wuraren shakatawa a fadin kasarta.

Firai Minista Jean Castex, ya bayyana wa Majalisar Wakilan kasar cewa matakin na daga cikin tsare-tsaren gwamnati na hana yaduwar cutar COVID-19.

Castex ya ce bayan sabbin dokokin da Shugaba Emmanuel Macron ya kaddamar a ranar Laraba, gwamnati ba za ta yi sanya ba wajen tarwatsa duk inda aka samu mutum fiye da shida a bakin kogi ko dandalin shakatawa.

Firai Ministan ya yi tir da masu saba dokokin kariyar cutar, bayan da aka yada hotunan wasu mutane suna shan giya a gefen wani rafi da tsakar rana a biranen Paris da Lyon.

Ya ba da umarnin yin bincike da kuma hukunta wadanda suka shirya casun da ya ce ya jefa rayuwar mutane cikin hadari.

Shugaba Macron ya ba da umarnin rufe makarantu te da umartar ma’aikata da su yi aiki daga gidajensu, a yunkurinsa rage yawan masu kamuwa da COVID-19 wanda ke kara nauyi a kan asibitocin kasar.

Sai dai bai wajabta zama a gida ko nisantar shiga taron jama’a ba.