✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Faransa za ta janye sojojinta daga Mali

Faransa da kawayenta za su yanke hukunci nan da tsakiyar watan Fabrairu kan janye dukarun.

Kasar Faransa tana duba yiwuwar ci gaba da zaman dakarun sojinta a Mali bayan gwamnatin sojin Malin ta kori Jakadan Faransa daga kasar.

Faransa da kawayenta za su yanke hukunci nan da tsakiyar wannan wata kan su janye dukkan dakarunsu ko
wani bangare na rundunar musamman da ake kira Operation Barkhane mai yaki da ’yan bindiga masu ikirarin jihadi a Mali.

Mali ta kori jakadan ne saboda abin da ta kira kalaman “ban-haushi” da Ministan Harkokin Wajen Faransa ya yi,
inda ya ce jami’an gwamnatin
sojin “ba halattattu” ba ne kuma “sun rasa abin yi.”

Tuni Faransa ta fara janye sojojinta kusan 5,000 da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.