✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kayan abinci ya soma sauka a Taraba

Sai dai har yanzu farashin shinkafa mai ɓuntu yana nan yadda yake.

Farashin kayan abinci ya soma faɗuwa a Jihar Taraba, lamarin da ke nuna cewa za a samu sauƙin tsadar rayuwa da ake fama ita.

A garuruwan Maihula, Mutum Biyu da Garba Chede da ke da manyan kasuwannin hatsi, binciken Aminiya ya nuna cewa farashin kayan abincin na ci gaba faɗuwa.

A garin Maihula, wani babban manomi, Ali Maihula ya shaida wa Aminiya cewa buhun masara mai nauyin kilo 100 da ake sayarwa kan Naira 54,000, a yanzu ya koma ana sayar da shi kan N40,000 zuwa N42,000.

Ya ce farashin buhun waken soya ya sauka daga N40,000 zuwa N32,000 sannan farashin dawa ya faɗi daga N50,000 zuwa N41,000.

Kazalika, ya ce farashin gero da farin wake da gyaɗa ya karye, sai dai har yanzu farashin shinkafa mai ɓuntu yana nan yadda yake.

Haka kuma, rahotanni daga garuruwan Mutum Biyu da Garba Chede sun nuna cewa farashin kayan abincin ya fara sauka.