✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fasinjoji sun rasu bayan motar haya ta fada a kogi

Motar haya ta fada a cikin kogi bayan barci ya dauke direba a cikin dare.

Mutum hudu sun bakunci lahira bayan motar haya da suke ciki ta kwace ta fada da su a cikin kogin ‘Black River’ da ke hade da Kogin Neja.

Masu aikin ceto sun yi nasarar tsamo gawarwakin mutum hudun, amma ba ga na biyar din ba, bayan faruwar lamarin a yankin Kotonkarfe da ke Jihar Kogi ranar Talata da dare.

Lamarin ya faru ne bayan direban motar hayar mai dauke da mutum 18, ya yi barci a yayin da yake tuki, motar kuma ta kwace ta yi cikin kogin da su.

Jami’an tsaron farin kaya na sibil defens da hukumar kiyaye hadura ta kasa ne suka yi aikin ceton, inda dauka ceto sauran fasinjojin su 13 a raye.

Kwamandan sibil difens na Jihar Kogi, Suleiman Mafara, ya ce sun yi aikin ceton ne bayan kiran neman dauki da suka samu daga jama’a.

Ya kara da cewa jami’an hukumar da sauran takwarorinsu na ci gaba da aiki domin gano ragowar fasinjan da ba a gani ba, gawarwakin kuma an wuce da su zuwa dakin ajiyar gawa da ke Lokoja.

Daga nan sai ya shawarci fasinjoji da direbodi da su rika kiyaye dokokin hanya domin kauce wa aukuwar hadura.