✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FBI ta bankado bayanan sirri 11 a gidan Trump

Trump ya yi zargin hukumomi da yunkurin ajiye wani abu a cikin gidan domin a kala masa sharri.

Jami’an Hukumar Leken Asiri ta Gwamnatin Amurka wato FBI, sun bankado wani ‘babban sirri’ da wasu muhimman takardu kan tsaron kasa a gidan tsohon Shugaban Kasar Donald Trump a Jihar Florida.

Hukumar FBI ta samu wasu bayanan sirri guda 11 a wani samame da ta kaddamar bisa umarnin kotu a gidan Trump.

Cikin takardun sirri da hukumar ta bankado har da muhimman bayanan sirrin kasar wadanda idan aka fallasa su a bainar jama’a, za su haifar da mumunar illa ga makomar Amurka.

Wata kotun tarayya ce ta ba wa jami’an FBI damar gudanar da bincike a gidan Donald Trump, kan zargin samun bayanan keta dokokin kasa guda uku, ciki har da adana bayanai da yadasu ko batar da wasu muhimman bayanai da suka shafi tsaron kasa.

Yadda FBI ta kai samame gidan Trump

Trump din kansa ne ya fara sanar da cewa FBI ta kai wani samame a wani katafaren gidansa da ke bakin teku a Jihar Florida, yana mai siffanta lamarin a matsayin rashin da’a.

Haka kuma, wani dan tsohon shugaban, Eric Trump ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News cewa, binciken da aka gudanar a gidan mahaifin nasa da ke Mar-a-Lago na da alaka da wasu takardu da ofishin adana takardun tarihi na Amurka ke nema ne.

Hukumar ta FBI dai ta kauce wa yin karin haske a kan samamen. To amma Trump wanda ba ya cikin gidan a ranar Litinin da daddare, a cikin sanarwar da ya fitar ya gaza fadin dalilin da ya sa jami’an suka ziyarci gidansa suka kaddamar da bincike.

Jaridar New York Times ta ambato tsohon shugaban na zargin ’yan siyasar jam’iyya mai mulki ta Democrat da tura masa jami’an FBI domin su bankado wani abu da zummar goga masa kashin kaji, ya samu matsala, a takarar shugabancin Amurka da yake honkoro a shekara ta 2024.

A watan Fabrairun da ya gabata rahotanni sun ce, an gano akwatuna 15 makare da muhimman takardun gwamnati da Mista Trump ya wuce da su gidansa maimakon ya bar su a Fadar White House.

So ake a kala min sharri —Trump

Mista Trump ya koka a kan yadda hukumomi suka hana shi sake shiga katafaren gidansa da ke bakin teku a Florida tun bayan samamen da jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI suka kai gidan.

Tsohon shugaban ya yi zargin hukumomi da yunkurin ajiye wani abu a cikin gidan domin a kala masa sharri.

Hakan na zuwa ne a yayin da Donald Trump din ya bayyana dazu a ofishin Atoni-Janar na birnin New York domin ya yi karin bayani a kan wata badakalar kasuwanci da iyalansa ke yi.

Sai dai Mista Trump ya yi biris yaki magana a ofishin domin ’yancin da yake da shi na dan kasa na ya yi magana ko ya yi shiru.

Kafin yanzu Trump din ya nemi kotu ta haramta gayyatarsa amma kotun ta ki aminta da hakan.

‘Babu dalilin raba takardun sirri da mazauninsu’

David Tafuri, wani tsohon jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, kuma babban lauya, ya ce da alama Mista Trump ya kwashi wasu takardun sirri da ba mallakinsa ba ne yayin da ya bar fadar Shugaban Kasa.

“Babu dalilin da zai sa a raba wasu takardun sirri daga mazauninsu, ko ma a ciro su daga cikin wani akwatin ajiyarsu na sirri.

“Tilas ne a bar irin wadannan takardu a wuraren da gwamnati ta tanada.

“Shi ya sa da zarar Shugabn Kasa ya sauka daga mukamin, daga wannan lokacin ba ya da damar daukar wani abu da ya kasance na sirri ne.”

Fadar White House ta ce ba a sanar da ita za a kai samamen ba sai bayan ya auku.