✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fira Ministan Birtaniya ya kamu da Coronavirus

Fira Minista Boris johnson na Birtaniya yana dauke da cutar Coronavirus. Mista Johnson ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa bai jima da fara jin…

Fira Minista Boris johnson na Birtaniya yana dauke da cutar Coronavirus.

Mista Johnson ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa bai jima da fara jin alamaun kamuwa ba.

“A sa’o’i 24 da suka wuce na dan fara jin alamu, kuma gwaji ya nuna cewa ina dauke da cutar Coronavirus”, inji shi.

Fira Ministan ya kuma ce tuni ya killace kansa, amma zai ci gaba da jagorantar yakin da ake yi da cutar ta hanyar sadarwa ta bidiyo.

A wani hoton bidiyo da ya wallafa tare da sakon kuma, Mista Johnson ya yi godiya ga ma’aikatan lafiya da ke fafutukar shawo kan annobar.

“Saboda haka ina godiya ga duk mutanen da ke yin abin da nake yi, wato aiki daga gida don a hana cutar yaduwa gida-gida—ta haka ne za mu yi nasara”.

Tun da farko dai wani mai magana da yawun Mista Johnson ya sanar da cewa Fira Ministan bay a jin dadi, don haka sakataren Harkokin Waje Dominic Raab zai rike masa kwarya.

A farko-farkon makon nan ne dai aka tabbatar da cewa Yarima Charles mai jiran gadon sarautar Birtaniya na dauke da cutar.