✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Flossie: Kyanwar da ta fi tsufa a duniya ta cika shekara 27

Kundin World Guinness ya tabbatar da shekarun kyanwara a matsayin mafi dadewa a duniya

Littafin Kundin Tarihi na Duniya (Guinness World Records) ya ce wata kyanwa mai suna Flossie, wadda aka haifa a 1995 a Ingila ita ce kyanwa mafi tsufa da take raye a duniya a yanzu.

Kyanwar wadda ta cika shekara 27 a jiya Alhamis kuma ta kafa tarihi, ta karbi takardar shaidar tabbatar da ita a matsayin kyanwa mafi tsufa a duniya ne a ranar 19 ga Nuwamban bana kamar yadda wata sanarwar kundin ta nuna.

Kundin Tarihin ya ce, an haifi kyanwa Flossie ce a ranar 29 ga Disamban, 1995, kuma zuwa ranar da aka ba ta takardar shaidar tana da shekara 26 da kwana 326.

Kundin Tarihin ya ce, shekarun Flossie “daidai” yake da kimanin shekara 120 na dan Adam.

Cibiyar kula da jin dadin kyanwoyi ta Cats Protection da ke Ingila ce ta mika bayanan kyanwa Flossie a watan Agustan bana don tantancewa.

Cibiyar dai tana kula da kyanwar mai launin baki da ruwan kasa ne, bayan da mai kula da ita ya sarayar da ikonsa na mallakarta.

“Mun ji mamaki lokacin da muka ga bayanan Flossie sun nuna ta kai kusan shekara 27,” in ji Naomi Rosling, shugabar reshen Cibiyar Cats Protection, a wata sanarwa.

Kyanwa Flossie tana zaune ne a cibiyar kasar Ingila. Bayanai sun ce Flossie tana cikin “koshin lafiya” duk da ba ta iya gani sosai kuma ba ta ji sosai, kamar yadda Kundin Tarihin ya bayyana.

ta don kula da ita. Green ta shaida wa Kundin Tarihin cewa kyanwar tana son wasa da kuma ‘halin dattaku.’

Ta bayyana kyanwar da ta musamman tun farkon ganinta, amma ba ta taba kawowa a ranta za ta kafa wannan tarihi na duniya ba.

Mamallakiyar kyanwar ta farko da ba a bayyana sunanta ba da ke aiki a asibitin Mereyside, bayanai sun ce ta tsince ta ce a kan hanya, inda ta kula da ita na shekara 10 kafin ta rasu ta bar kyanwar.

’Yar uwar marigayiyar ta ci gaba da kula da kyanwar inda suka shafe shekara 14 kafin ita ma ta rasu ta bar ta.

Kyanwar da ta zama marainiya har sau biyu, ta koma karkashin kulawar dan mai kula da ita ta karshe na tsawon shekara uku kamar yadda Kundin Tarihin ya nuna.

Dan ne ya mika kyanwar ga Cibiyar Cats Protection bisa fatar ta samu kulawar da ta fi dacewa.

Ba kyanwa Flossie ce kawai karamar dabbar gida da ta shiga Kundin Tarihin ba a wannan wata.

Kundin ya bayyana wani kare da ya fi tsufa a duniya, wanda dan asalin yankin Eskimo na Amurka ne da yake da ruwan Chihuahua mai suna Gino Wolf da ke birnin Los Angeles.

Kare Gino, mai shekara 22, ya karbi takardar tantance shi a ranar 15 ga Nuwamban bana kamar yadda Kundin Tarihin ya bayyana.