Ganduje ya sa hannu a sabon kasafin kudin Kano | Aminiya

Ganduje ya sa hannu a sabon kasafin kudin Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
    Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a kan kasafin kudin 2020 da aka yi wa gyaran fuska da ya haura Naira biliyan 138 a jihar.

Gwamnan ya rattaba hannun ne a wani kwarya-kwaryan biki da ya gudana a fadar gwamnatin jihar a ranar Alhamis.

Kwaskwarimar dai ta biyo bayan ragin da aka samu a kudaden shigar jihar saboda annobar COVID-19.

A cikin sabon kasafin kudin dai, jihar ta zaftare kimanin kaso 30 cikin 100 na Naira biliyan 200 da aka amince tun da farko.

“Muna sane da cewa annobar COVID-19 ta tilasta rufe jiharmu na sama da wata daya wanda hakan ya yi matukar illa ga hanyoyin kudaden shigarmu da kuma abin da muke samu daga lalitar gwamnatin tarayya.

Da haka ne muka ga ya kamata mu sami kasafi na gaskiya da zai dace da halin da muke ciki”, inji Ganduje.

A sabon kasafin kudin dai, an ware Narira biliyan 78 da miliyan 800 domin ayyukan yau da kullum, yayin da manyan ayyuka za su lakume Naira biliyan 54 da miliyan 900.

Ganduje ya ja kunnen dukkan ma’aikatu, hukumomi da bangarorin gwamnati da su kara rubanya kokarinsu don tunkarar kalubalen bayan annobar COVID-19 a jihar.