Ganduje ya ziyarci Fadar Sarkin Warri | Aminiya

Ganduje ya ziyarci Fadar Sarkin Warri

    Ishaq Isma’il Musa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya kai ziyarar ban girma Fadar Sarkin Warri, Olu Ogiame Atuwatse III.

Ganduje wanda ya ziyarci Jihar Delta a ranar Litinin domin jajanta wa iyalan marigayi Birgidiya-Janar Dominic Oneya (mai ritaya) ya kuma ziyarci Masarautar ta Warri.

Marigayi Janar Dominic wanda ajali ya katsewa hanzari makonni biyu da suka gabata, da daga cikin manyan jami’an da suka rike madafan iko na jagorancin Jihar Kano a lokacin mulkin soja.

Bayan ta’aziyyar ce gwamnan ya ziyarci masarautar inda Sarkin ya yi masa kyakkyawar tarba har suka sha hotuna.