✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai biya kudin karatun daliban Kwankwasiyya miliyan N258

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira miliyan 257.2 domin biyan kudin karatun daliban Jihar 43 da ke karatu jami’o’i a kasar Masar. Gwamna Abdullahi Ganduje…

Gwamnatin Jihar Kano ta ware Naira miliyan 257.2 domin biyan kudin karatun daliban Jihar 43 da ke karatu jami’o’i a kasar Masar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce ya yara da biyan kudin karatun daliban domin kyautata rayuwarsu, duk da cewa wasunsu sun tsoma kansu a cikin harkokin siyasa.

Daliban sun hada da 37 masu karatu a Jami’ar Mansoura da wasu guda shida da Jami’ar Octobe 6 a kasar Masar.

Idan ba a manta ba batun daliban ya haifar da cacar bakin siyasa  tsakanin Gwamantin Ganduje da ta magabacinsa Rabiu Musa Kwankwaso da ta fara fice wajen daukar nauyin daliban jihar su yi karatu a kasashen waje.

Sanarwar mai magana da yawun Gwamna Ganduje, Abba Anwar,

Ya fitar ta ce, “Bara Gwamna Ganduje ya yi afuwa ga dalibai 37 masu karatu a Jami’ar Mansoura ya kuma biya Naira miliyan 209,596,633.00k na kudin karatunsu da ake bin su bashi.

Abba ya ce dukkannin daliban sun rubuta takardar neman afuwar gwamnan kan abin da suka yi masa ba daidai ba.

Ya ce jihar ta ta yi alkawarin kara wa daliban alawus din da take ba su.