✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gandun kiwon Dukku a Gombe zai rage rikicin manoma da makiyaya’

Dajin dai na aka kammala shine zai kasance irinsa mafi girma a Najeriya.

An bayyana cewa samar da gandun kiwo ga makiyaya da Gwamnatin Tarayya ta ke ginawa a Wawa Zange da ke Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe zai rage rikicin manoma da makiyaya a yankin.

Jami’in Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya (FMARD) dake Gombe Dokta Musa Inuwa, ne ya bayyana hakan a Gombe ranar Juma’a.

Ya ce da zarar an kammala, aikin zai samar da dabbobi sannan zai rage yawan kaura da makiyaya ke yi daga Arewaci zuwa Kudancin Najeriya domin kiwo.

Jami’in ya ce akwai ayyuka guda shida da yanzu haka ake gudanarwa a dajin tun daga shekarar 2020, da suka hada da samar da ruwa.

Dokta Musa ya kuma ce an ware kadada 10 domin noman ciyawa tare da gina asibitin dabbobi da na mutane da kuma hanyoyi.

A cewar sa, asibitin mutane yanzu haka ya kai kaso 100 da kammalawa, yayin da asibitin dabbobi kuma kashi ya kai kaso 70, sai kuma madatsar ruwa da ta kai kaso 80 zuwa 90 cikin 100.

A bangaren hanya kuwa, jami’in ya ce ta kai kimanin kaso 30, shuka ciyayi kuma bai wuce kashi 50 cikin 100 ba saboda sai damuna ta kankama saboda gudun asarar irin ciyarwa da kuma taki.

Dajin, a cewarsa shine mafi girma a Najeriya inda fadinsa ya kai kadada 141,000 kuma ya hade Kananan Hukumomi hudu na Jihar da suka hada da Dukku da Kwami da Funakaye da Nafada.

Aminiya ta gano cewa Gwamnatin Tarayya a shekarar 2020 ta ware makudan kudade har Naira biliyan 2.5 don inganta wannan daji na Wawa zange.