GANI YA KORI JI: Hotunan zanga-zangar Kungiyar Kwadago kan yajin aikin ASUU | Aminiya

GANI YA KORI JI: Hotunan zanga-zangar Kungiyar Kwadago kan yajin aikin ASUU

    Abdullahi Abubakar Umar
A ranar Talata Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta fara gagarumar zanga-zangar kwana biyu a fadin kasar kan yajin aikin jami’o’i da ya ki ci ya ki cinyewa.
Hotunan yadda zanga-zangar ke gudana a wurare daban-daban.

Dubban mutane sun halarci zanga-zangar domin mara wa kungiyar ASUU baya a Kano. Hoto: Salim Umar Ibrahim.

Yadda zanga-zangar NLC ta shirya kan yajin aikin ASUU ke gudana a Kano. 📷: Salim Umar Ibrahim

 

Dandazon masu zanga-zangar da NLC ta kira a Legas a ranar Talata. 📷: Benedict Uwalaka

A Ibadan da mutane sun yi fitar farar dango zuwa kan titina domin zanga-zangar da NLC ta shirya kan yajin aikin ASUU. 📷: Jeremiah Oke

Tun da sanyin safiyar Talata, mambobin kungiyyoin da NLC ke jagoranta suka fito domin gudanr da zanga-zangar a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. 📷: Magaji lsa Hunkuyi

Yadda zanga-zangar da Kungiyar Kwadago ta shirya kan yajin aikin ASUU ke gudana a garin Jos. 📷: Dickson Jos