Gatarin zalunci a kan Sanusi Lamido Sanusi | Aminiya

Gatarin zalunci a kan Sanusi Lamido Sanusi

A yayin da muke zaune a wani lambu muna hutawa, kawai sai gardama ta sarke tsakanin Habu Mai Kunya da abokinsa Dauda kulu dangane da labarin da ya cika gari, wato na dakatar da Sanusi Lamido Sanusi daga mukaminsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya. Muhawara a tsakaninsu ta sarke, kowa ya dauki bangarensa. Ni kuwa da yake dan rahoto ne, sai na nade dukkan abin da ya wakana a tsakaninsu kuma ga yadda ta kwashe:
Habu Mai Kunya: Ni kam ina ganin abin da ya yi wa Sanusi Lamido Sanusi, Jonathan ya daba wa cikinsa wuka ne kuma ya buga kirari. Idan ba haka ba, yaya za ka fassara wannan kasassaba, tun da watanni uku kacal suka rage masa ya kammala wa’adinsa?
Dauda kulu: Ni kam ina ganin Jonathan ya yi daidai da ya kori Sanusi, domin kuwa shi mutum ne mai jiji-da-kai, marar ladabi ga manya.
Habu Mai Kunya: Kana nufin ba ya yin ladabi ga barayi? Ina jin kamata ya yi jami’in gwamnati ya kasance mai yin hidima ga al’ummar kasarsa amma ba ga wasu mutane can ba.
Dauda kulu: Ka fadi duk abin da za ka fadi, ni dai na san cewa bai yiwuwa a samu shugabannin kasa biyu a kasa daya. Idan ka lura, Sanusi Lamido ya dauki kansa kamar wani Shugaban kasa ko kuma wani abu da ya fi haka.
Habu Mai Kunya: Wa ya gaya maka cewa ba za a iya samun shugabannin kasa biyu a kasa daya ba? A yanzu haka shugabannin kasa guda hudu muke da su a ksar nan. Ga su: Na daya, Jonathan. Ta biyu, matarsa, Patience. Ta uku, Ministar Fetur, Dizeni Alison-Madueke. Sai kuma na hudu, Edwin Clark.
Dauda kulu: Ka ji ka, wannan sharri ne kawai da bata suna.
Habu Mai Kunya: Sam, wannan ba sharri ba ne ko bata suna. Ni dai ban san abin da kake amfana da shi ba da kake goyon bayan wannan gwamnati mai ciyar da al’umma baya. Kuna ba ni mamaki da kuke ingiza Jonathan kuna sanya shi yana karfafa wa barayin dukiyar gwamnati gindi, a gefe daya kuma yana korar mutanen kirki masu gaya masa gaskiya daga gwamnatinsa.
Dauda kulu: Ya isa haka nan, ko za ka gaya mani wace sata ko barayi kake nufi? Kana nufin shi kansa Sanusi ba barawo ba ne? Ko ka samu damar karanta rahoton Majalisar ’Yan Rahoton Al’amuran Kudi, inda suka bayyana dalla-dalla yadda ya tafiyar da aikinsa? Sun gano yadda ya gudanar da aikinsa cikin sakaci da bahallatsa da karya doka da wuce-gona-da-iri.
Habu Mai Kunya: Kafin a dauki wannan mataki a kansa, ina wannan rahoto ya makale? Ka gani ko? Matsalar Jonathan din nan ita ce, ya dauki mutane kamar wawaye. Idan da an tabbatar da cewa Sanusi Lamidio barawo ne, da tuni an hukunta shi, amma sai yanzu za a fake da wani rahoto? Ke nan sun danne wani bayani ne da nufin su yi amfani da shi domin su rufe masa baki, amma da suka ga cewa ya jajirce kan gaskiya sai suka kore shi sannan suka shafa masa kashin kaji, domin bata masa suna a idon jama’a. Wane ne ma zai amince da zancen Shugaban kasar da ya kewaye kansa da mutanen da suka yi kaurin suna wajen sata? Shugaban da aka sani da yi wa gaggan barayi ahuwa?
Dauda kulu: Ka ji abin da kake fada ko? Wannan ya nuna kai ba mai kishin kasa ba ne. Mene ne laifi ga Jonathan don ya yi amfani da damar da doka ta ba shi na yi wa fursunoni ahuwa? Ko kuwa don kawai ya fito daga yankin Kudancin Kudun Najeriya, shi ya sanya ake yi masa gani-gani, ake yi masa tsageranci?
Habu Mai Kunya: Bari in amsa maka tambayarka da wata tambayar – Shin don Sanusi Lamido ba dan Kudancin Kudun Najeriya ba ne, shi ya sa ya sauke shi daga mukaminsa, kawai don ya tona asirin almundahana?
Dauda kulu: Ya kamata ka san cewa shi fa Shugaban kasa babu ruwansa da wani mutum shi karan kansa, amma ya damu ne da yadda hukumomin gwamnati ke gudana. Yana son ne ya ga cewa Babban Bankin Najeriya ya zama ingantacce, ba wai a rika amfani da shi a siyasa ba, kamar yadda Sanusi Lamido ya yi.
Wannan tattaunawa ba ta kare ba, a biyo mu mako mai zuwa, domin jin yadda ta kaya tsakanin Abu Mai Kunya da abokinsa Dauda kulu.
Za mu ci gaba