✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gidajen da iska ta yi wa barna sun rabauta da tallafi a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba kimanin buhuna 300 na hatsi a matsayin kayan tallafi ga iyalai kimanin 638 wadanda ruwa da iska suka yi wa…

Gwamnatin Jihar Kebbi ta raba kimanin buhuna 300 na hatsi a matsayin kayan tallafi ga iyalai kimanin 638 wadanda ruwa da iska suka yi wa ta’adi a Birnin Kebbi a watan da ya gabata.

Babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Sani Dodo shi ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayan tallafin a Birnin Kebbi.

Ya ce gwamnatin ta raba tallafin ne domin ta rage musu radadin iftila’in, ko da yake hukumar ba ta fadi hakikanin yawan kudin da ta kashe wajen raba tallafin ba.

Jami’in ya ce sun yi amfani da masu rike da sarautun gargajiya wajen tattar bayanan wadanda suka ci gajiyar tallafin.

“Hukumarmu ta raba buhunan shinkafa guda 60, na masara 60, dawa 60, gero 60, shinkafa 300, tirela daya ta siminti domin gine-gine sai bandur 100 a kwanon rufi”, inji shi.

Sauran kayayyakin da hukumar ta raba sun hada da fallen sili guda 200, kusoshin rufi buhu 40 da kuma wasu buhuna 40 din na kusa inci uku.

A makon da ya gabata ne dai wani ruwa da iska mai karfi ta lalata akalla gidaje 300 a anguwannin Badariyya, barikin ‘yan sanda, Bayan Kara da wani bangare na Gesse III dake Birnin Kebbi.