✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta cinye shugana a kasuwar sansanin alhazai ta Kano

Wata ’yar kasuwa ta ce ba a fitar da ko kyalle daga kantinta ba a gobarar

Gobara ta kone shaguna a Kasuwar Sansanin Alhazai da ke Kano, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar kaya na makudan kudade.

Daya daga cikin ’yan kasuwar da iftila’in ya shafa, Hajiya Aisha Abduljalal, ta bayyana cewa ko da aka kira ta ta iso kasuwar, ta tarar da shagonta yana ci da wuta, kuma ba a a fitar da ko kyalle daga ciki.

Shugaban kasuwar ta sansanin alhazai, Alhaji Auwalu Ahmad Shinkafi, da yake tabbatar da konewar shaguna hudu a gobarar, ya ce, “Ana tunanin gobarar ta tashi ne sanadiyyar matsala ta wutar lantarki, kuma mu kanmu ba mu san adadin dukiyar da aka yi asara ba.

“Maganar da muke fa muna magana ne a kan asarar milyoyin Nairori, za mu sanar da ku idan muka iya tantace asarar nawa aka yi.

“Mun kira ma’aikatan kwana-kwana da ma sauran hukumomi kuma sun ba mu gudummuwarsu sosai domin shawo kan iftila’in” inji Alhaji Auwalu.

Aminiya ta gano cewa gobarar ta da fara ci da misalin karfe 7 na daren ranar Juma’a ta cinye kayan sawa na mata a shagunan.

Da yake tabbatar da faruwan lamarin, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, ya bayyana cewa sun samu kai dauki a wurin da abin ya faru bayan sun samu kiran waya, wanda hakan ya ba su damar shawo kan gobarar.