✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a gidan Sheikh Ahmad Gumi

Gobara ta tashi a gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi. Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne ranar Asabar…

Gobara ta tashi a gidan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne ranar Asabar da tsakar rana.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton dai babu cikakkun bayanai kan musabbabin gobarar ko yanayin ta’adin da ta yi, amma wasu ganau sun ce ta kone saman rufin gidan, kafin daga bisani mutane su taimaka wajen kashe ta.

Kazalika, ana amfani da wani sashe na gidan a matsayin makaranta.

Malamin dai ya tabbatar da faruwa lamarin inda ya ce, “Wannan gobarar daga Allah take, kuma ba za mu iya cewa ga abin day a kawo ta ba, saboda babu wutar lantarki lokacin da ta faru.

Bugu da kari, an wallafa bidiyon gobarar a shafin malamin na kafar sada zumunta na Facebook, yayin da matasa ke kokarin kashe ta, saboda kada ta ci gaba da kama wasu sassan gidan.