✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri

A bara ma an samu irin wannan ibtila’i na aukuwar gobara a Kasuwar Gomboru.

Wata gobara ta ƙone wasu sassa na shahararriyar Kasuwar Gomboru da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Bayanai sun ce gobarar dai ta tashi ne a ɓangaren ’yan Katako da ke cikin kasuwar inda ake sayar da itace da kayan kafinta.

Wani ganau da ke wurin ya ce zuwa yanzu ba za a iya tantance barnar da gobarar ta yi ba amma an shawo kan lamarin.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 9:50 na dare, inda shaguna da dama suka ƙone a lokacin da jami’an kashe gobara suka isa cikin ta ‘yan mintuna.

Aminiya ta ruwaito cewa ɗaukar matakin gaggawa ya taimaka wajen kashe gobarar.

A bara ma Kasuwar Gomboru dai ta sami irin wannan bala’i na tashin gobara.

Har ya zuwa kammala wannan labari ba a iya tantance musabbabin barkewar gobarar ba kana ba a kai ga kididdige barnar da ta yi ba.