✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi mummunan ta’adi a kasuwar babura a Sakkwato

Ba za mu iya kididdige adadin baburan da gobarar ta kone ba a yanzu.

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Jihar Sakkwato da safiyar yau Litinin ta yi sanadiyar ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.

Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin cewa gobarar ta tashi ne daga wata ’yar juji da ke cikin kasuwar.

Shugaban kungiyar masu sayar da babura, Shehu Muhammad ya shaida wa wakilinmu cewa gobarar ta lalata babura da dama.

“Ba za mu iya kididdige adadin baburan da gobarar ta kone ba a yanzu saboda wutar na ci gaba da ruruwa.

“Amma mutane da yawa sun yi asarar shagunansu tare da baburan da ke ciki saboda ba su iya zuwa kan lokaci bayan tashin gobarar da misalin karfe 6 na safiyar yau.

Shehu ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai masu ɗauki domin “kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba.” in ji shi.

Shi ma Honarabul Ibrahim Muhammad Giɗaɗo, mai bai wa gwamna shawara kan babbar kasuwar ya ce wutar ta tashi da sanyin safiyar yau.

Ya ce “ɓangaren da ya ƙone sosai a cikin kasuwar shi ne na ’yan mashin da kekuna, ana iya samun shago guda ɗauke da mashin fiye da 200 ko 100, shagunan gaba ɗaya sun ƙone.

“Waɗannan mashina akwai waɗanda suka haura miliyan, akwai asara mai yawa,” a cewarsa.

Giɗaɗo ya ƙara da cewa jami’an kashe gobara sun kashe kashi 80 cikin 100 na gobarar da ke ci.