✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gombe: Kotu ta daure hadimin Goje kan taba shugabannin APC a Facebook

A ’yan kwanakin nan dai, dangantaka ta yi tsami tsakanin Goje da gwamnatin Jihar.

Wata kotun Majistare a Jihar Gombe ranar Talata, ta ba da umarnin tsare wani hadimin Sanata Danjuma Goje a gidan gyaran hali.

Kotun dai ta ba da umarnin ajiye shi ne saboda wallafa wani sako a shafinsa na Facebook kan shugabannin APC a Karamar Hukumar Yamaltu/Deba ta Jihar.

Ana dai gurfanar da mutumin, Muhammad Adamu Yayari, wanda hadimi ne ga Sanatan kan kafofin sada zumunta na zamani, a gaban kotun bayan Sakataren APC na Jihar, Abubakar Umar S. Goro ya yi korafi a kansa.

An dai kama hadimin ne tare da tsare shi a hedkwatar ’yan sanda ta Jihar ranar Litinin.

A cewar takardar tuhumar kotu a kan hadimin, ana zarginsa ne da cewa a ranar 25 ga watan Nuwamban 2021, ya wallafa wani sako da zai iya cutar da shugabancin jam’iyyar a Yamaltu/Deba a shafinsa na Facebook.

Lauyar Gwamnatin Jihar, Ramatu Ibrahim Hassan, wacce ta karanta kunshin tuhumar, ta ce ikirarin da ya yi cewa kaso 80 daga cikinsu sun ajiye mukamansu, babu kamshin gaskiya a ciki.

Ta shaida wa kotun cewa laifin da ya aikata ya saba da sassa na 393 da na 114 na kundin dokar Penal Code.

Da aka tambayi wanda ake zargin ko gaskiya ne tuhumar da ake masa, ya musanta aikata hakan.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Mohammed Sulaiman Kumo, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar shida ga watan Disamba domin duba yiwuwar ba da belinsa.

Sai dai kafin nan, kotun ta umarci a ajiye shi a gidan gyaran hali.

Aminiya ta rawaito cewa gurfanar da hadimin ya biyo bayan sakon da ya wallafa kan shugabannin a ranar Alhamis kan ajiye mukaman nasu.

A ’yan makonnin nan dai, dangantaka ta yi tsami tsakanin tsohon Gwamnan Jihar, kuma Sanata mai ci, Danjuma Goje da kuma Gwamnan Jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.