✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwagwarmayar da muka sha kafin kafa Bankin Jaiz —Hassan Usman

Idan mun sayi kaya kamar a N10m sai mu ce to mun sayar maka a kan N12m kuma za ka biya mu a shekara daya.

A kwanakin baya ne Bankin Jaiz ya cika shekara 10 da kafuwa. A kan haka Aminiya ta tattauna da Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwar bankin wanda shi ne Bankin Musulunci na farko, Malam Hassan Usman game da yadda aka faro tafiyar bankin.

Shekara goma da kafuwar Bankin JAIZ yaya aka yi ya kafu har ga shi ya cika shekara 10?

Gaskiya shekera 10 shi ne lokacin da aka bude bankin aka fara hada-hada.

Amma maganar Bankin JAIZ ta faro ne shekara goma kafin nan wato tun shekarar 2003 aka nemi hannun jari, don neman izinin kafa Bankin Musulunci na kasa amma bai yiwu ba, aka yi ta samun canje-canje,wanda hakan ya kawo tsaikon samun lasisin bude bankin.

Amma duk wasu sharudda da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shimfida mun cika su.

Haka aka yi ta jan kafa har Allah Ya kawo Sarkin Kano na 14 Malam Muhammadu Sunusi, ya yi gyare-gyare a ka’idojin kafa bankin inda ya sassauta wasu dokoki hakan ta sa aka kafa wannan banki na JAIZ a shekarar 2012.

An fara gudanar da bankin a watan Janairun shekarar 2012 tare da bude rassa uku a Abuja da Kaduna da Kano.

Kamar yadda kuke alakanta bankin da Bankin Musulunci, akwai bankin da ake kira BCCI wadda ya fuskanci kalubale kasancewar ana alakanta shi da Musulunci, kana ganin irin wancan kalubale da bankin ya samu, ba zai kawo muku nakasu ba, lura da irin halin da muke ciki a kasar nan?

Akwai bambanci domin duk duniya ko a Faransa da Ingila da Amurka kai duk Turai an san irin wannan banki na Musulunci (Islamic Bank), domin abin da ake nufi da bankin Musulunci shi ne tafiyar da hada-hadar kudi ba tare da riba ba.

Kuma sai ya kasance Musulunci ne ke kan gaba wajen yaki da riba, hakan ta sa ake gudanar da Bankin Musulunci duk da cewa sauran addinan nan biyu wato addinin Yahudu da na Nasara duk littatafansu na cewa riba ba ta da kyau.

To duk da cewa mabiya wadancan addinan na da dan sassauci a kan wannan lamari na riba amma Musulunci ba ya da wani gurbi na yin sassauci a kan haramcin riba.

Kuma a sani cewa irin wannan banki na Musulunci ba a nan aka fara ba, akwai kasashen da ke da bankunan da ba ruwa a cikinsu.

Kuma za ka tarar da ka’idojin da aka tsara su na abin da ya shafi hadahadar kudade na cinikayya wadanda dukkan addinai suka yarda da su ne don a kauce wa abubuwan da za su cutar da mutum.

Kuma ko cikin cinikayyar akwai daidaito, kuma kada a boye wani abu.

Ka san Musulunci ya yi hani da in za ka sayar da abu ka boye aibinsa. Ai ka ga dukkan addinai sun yarda da wannan tunda adalci ne a ciki.

Kuma rashin fahimta ce ke sa mutum ya ki wannan domin ga misali mutum ne sai ya zo Bankin JAIZ ya ce yana son bashi za mu tambaye shi me zai yi da kudin?

In ya ce zai sayi gida ne, za mu tambaye shi cewa ina gidan domin mu ne ke sayen gida mu ba shi haya wanda tun yana haya har zai kai ga mallakarsa, a hankali har ya zama nasa, ko kamfani ne yake zuwa ya sayo haja ya sarrafa to sai mu sayo hajar da kanmu, mu sayar masa da ribar mu a kai.

Misali tunda harka ce ta kasuwa idan mun sayi kaya kamar a Naira miliyan 10 sai mu ce to mun sayar maka a kan Naira miliyan 12 kuma za ka biya mu a shekara daya.

Wannan sabanin mutum ya je banki kudin da za su ba shi don ya yi wata sayayya sai sun dora masa ruwa na wani kaso mai yawa, kuma wa’adin da aka diba masa na dawowa da kudin idan ya yi bai biya, a kullum kudin na kara hawa ne.

Kamar da jarin nawa JAIZ ya fara?

Tun 2003 jarin da za a iya bude banki da shi Naira biliyan biyu da rabi ne, amma a wannan lokaci muna jarin da ya haura abin da ake bukata, sai dai da Allah bai yi ba, ba mu samu lasisi ba har sai da hannun jarin ya kai Naira biliyan 25.

Allah cikin ikonSa da aka samar da sabbabin ka’idoji, aka rage kudin zuwa Naira biliyan 5, amma shi ma lasisi ne, mai gajeren zango, domin za a iya bude rassa ne kawai a shiyoyi 2 daga cikin shiyya 6 da muke da su a kasar nan.

To sai muka fara da shi wannan gajeren lasisi sai da muka shekara hudu, kafin muka kara hannun jari ya koma Naira biliyan 10 wanda da shi ne za ka iya yin harkar banki a ko’ina a Najeriya.

Don haka a yanzu lasisinmu muna da ikon bude reshe a ko’ina a fadin kasar nan. A yanzu haka kuma muna da jarin da ya kai Naira biliyan 23.

Ko akwai wadanda ba Musulmi ba da suke hulda da ku, kuma suke da hannun jari a wannan banki?

Lalle akwai masu harka da wannan banki da ma’aikatan banki da ba Musulmi ba suna nan da yawa.

Ai kamar yadda na ce shi harkokin kasuwanci misali in ka je Kasuwar Wuse ko Kwari ko Sabon Gari a Kano ko wata kasuwa a Legas ko Enugu da sauransu ai ba za ka ce sai a hannun Musulmi ko Kirista za ka sayi kaya ba, muddin mutum ya gane maganarka shi ke nan a hannunsa za ka saya.

Don haka Bankin Musulunci kasuwa ce ka saya ka saida ko kuma ka zo mu hada hannu mu sayi kayan mu saida.

Ba ma bambanta Musulmi da wanda ba Musulmi ba, haka ma’aikatanmu ba ma banbanta Musulmi da wanda ba Musulmi ba.

Harkar kasuwanci akan samu riba, wata rana akasin haka, ko kun taba cin karo da wasu matsaloli makamantan haka?

Haka ne lallai ita harkar banki tana tattare da haka, amma a bangarenmu lokacin da muka fara shekara ta daya zuwa biyu maimakon a samun riba sai muka samu akasi, amma a shekara ta uku mun fara samun dacewa zuwa yanzu babu abin da za mu ce sai mu gode wa Allah (SWT) kasancewar mun samu ci gaba mai yawa.

Kuma mun bunkasa don a yanzu haka muna da rassa kimanin 40 a fadin kasar nan har da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A kwanan nan bankinku ya hadu da wata takaddama game da sake gina Kasuwar Jos a Jihar Filato, inda aka samu turjiya daga wasu mutane ciki har da Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) suka nuna kin amincewarsu na ku sake gina kasuwar. A yanzu wane hali ake ciki?

Shi wannan abu na gina Kasuwar Jos zan iya cewa wani abu ne da ya faru na rashin fahimta koda yake ba zan ce babu matsaloli a Jos na zamantakewa ba, akwai su kowa ya sani.

Kuma musamman mutanen da suke da fahimta da kunya a ce sun fito da wadannan irin maganganu saboda ba maganganu ne na wadanda suke son ci gaban kasa ba, domin duk mai kishin kasa ba zai fito ya kalubalanci abin da zai amfani jama’a, ya rufe ido ya ce sam wannan abin ba zai yiyuwa don son zuciyarsa.

Tunda Mai girma Gwamnan Jihar Filato mutum ne mai son ci gaban al’umma fatarmu ita ce ya wayar da kan jama’arsa dangane da fa’idar da ke akwai gare su a kan kokarin gudanar da wannan aiki.

Kuma mu a kullum manufarmu ita ce ta yaya za mu taimaki jama’a musamman na kasa ta yadda za su samu jarin da za su iya tsayawa da kafafunsu a harkokinsu na kasuwanci ta bin hanyoyi masu tsabta.

Da yawa cikin jama’a sun jahilci manufar wannan banki, wadanne hanyoyi kuke bi don wayar da kansu su san alheri da fa’idojin da ke tattare da bankinku na JAIZ?

To a gaskiya babu wata kafa da muka bari don wayar da kan jama’a walau a jaridu ko rediyo da talabijin ko kafofin yada sada zumunta.

Wace hanya mutum zai bi don neman banki ya saya masa gida ko abin hawa ko a ba shi kudi wadanne ne ka’idojinku?

To ka’ida ta farko ita ce, kamar yadda Bankin CBN ya tanada, sai ka bude asusun ajiya a banki ta yadda kudade suna shiga suna fita.

Akwai kwarent, wanda shi ne asusun ajiya na yau da gobe da za ka iya ajiya don gudanar da harkokin kasuwancinka, kuma za ka iya dauka a duk lokacin da kake bukata.

In kuma kai ma’aikaci ne kake son shiga bankin don samun amfaninsa za a ce ka kawo albashinka wannan banki tare da duba nawa ne albashin a duk wata, kuma in an duba albashinka ya kai minzanin za a iya ba ka gida ta yadda za ka iya biya wata-wata ba tare da wata matsala ba, to ta haka ne za a duba a ga za ka iya samun lamuni daga wajenmu.

Haka in mota kake so ka saya sai a duba motar ta yi, to sai kuma a duba nauyin albashinka mu ga kamar za ka iya biyan cikin shekara uku, kuma in kamar motar an saye ta ce a kan Naira miliyan uku to za ka biya mu kamar miliyan uku da rabi ya danganta da yadda lamarin yake.

Misalin na bude asusun ajiya a bankinku, kuma ya kasance na cika sharuddan wane lokaci za a iya dauka don ba ni lamuni?

To ya danganta in kai sabon zuwa ne sai ka yi kamar wata 6 mun ga kamun ludayinka kafin mun amince da ba ka lamuni in kuma kai ma’aikacin gwamnati ne matukar albashinka ya shiga sau biyu ko uku to a nan za mu iya ba ka lamuni.

Idan mutum ya kasance lamunin da yake so ba gida ba ne ba mota ba kasuwanci yake son yi da shi ta yaya zai amfana?

Za mu ga wane irin kasuwanci kake da shi misali in kamar shadda kake sayarwa, to sai mu ga a wajen wa kake saye, in kana sayen kamar ta Naira miliyan 5 ne sai ka nemi lamuni, sai mu je wajen wanda kake kasuwanci da shi mu kara kudin da ka nema kamar daga miliyan 5 da a baya kake saya ya koma Naira miliyan 10 wato an ba ka lamunin miliyan 5 ke nan, ka ga ai jarin ya bunkasa, kuma za ka biya a wata 12.

A karshe wane kira za ka yi ga masu mu’amala da wannan banki naku?

Da farko ina godiya da san barka ga abokan huldarmu dangane da yadda suke ba mu hadin kai, saboda a gaskiya kullum za ka tarar da masu hulda da mu suna ci gaba da bunkasa kuma muna kara samun abokan hulda.

Don haka muna gode musu da hakan kasancewar wadanda suke hulda da mu suna samun gamsuwa lura da cewa harkar banki ne da babu ruwa a ciki.

Kuma muna ba su tabbacin ci gaba da gamsar da su ta kowace fuska.