✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Ondo ya sallami kwamishinoni da masu ba shi shawara

Gwamnan ya umarci kwamishinonin da su dawo da duk kayan gwamnaitin da ke hannunsu

Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya sallami daukacin kwamishinoni da hadimai da masu ba shi shawara nan take. 

Gwamnan ya kuma umarci kwamishinonin da su mika duk kayan gwamnaitin da ke hannunsu ga Manyan Sakatarorin ma’iakatun ko kuma jami’ai mafiya girman mukami.

“Gwamnan yana umartar wadanda wannan mataki ya shafawa da su dawo da duk kayan gwamnati da ke hannunsu,” in ji sanarwar rushe majalisar kwamishinonin da sallamar hadiman da sakataren yada labaran gwamnan, Prince Ebenezer Adeniyan, ya fitar.

Sanarwar ta kara da nuna godiyar Gwamna Aiyedatiwa a gare su, kan hidimar da suka yi wa jihar.

Wannan mataki na zuwa ne makonni uku da zaman Aiyedatiwa gwamnan a sakamakon rasuwar mutuwar fuju’ar Gwamnan Rotimi Akeredolu wa watan Disamba.

Kafin rasuwar Akeredolu dai dangantaka ta yi tsami tsakansin su, har ta kai ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya baki, amma duk da haka, haka ba ta cim- ma ruwa ba.