✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta bukaci a kara kaimi wurin yaki da safarar mutane

Hukumar NAPTIP mai yaki da safarar mutane ta Najeriya ta kama mutum 4,215.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci jama’a su kara jajircewa wurin yaki da safarar mutane da nufin kassara masu aikata muggan laifuka a Najeriya.

Wakilin Ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan Yaki da Aikata Muggan Laifuka da Shaye-shayen a Najeriya (UNODC), Oliver Stolpe, ya yi kiran a taron masu ruwa da tsaki kan yaki da safarar mutane a kasar daga 2021 zuwa 2025, wanda UNODC da hadin guiwar ofishin jakadanci kasar Swizerland a Najeriya suka shirya.

Mista Oliver, ya yaba wa Gwamnatin Najeriya saboda yin tsayin dakarta wurin yaki da safarar mutane a fadin kasar amma ya ce, har yanzu akwai bukatar toshe hanyonyin da masu aikata laifin ake amfani da su.

Ya ce kawo yanzu hukumar NAPTIP mai yaki da safarar mutane ta Najeriya ta yi nasarar kama mutum 4,215 da ake zargi a fadin kasar.

Mai ba da shawara kan ‘yan gudun hijira a Ofishin Jakadancin Switzerland a Najeriya, Manuel Muhlebach, ya ce, “safarar mutane babbar barazanar tsaro ce da take addabar rayuwar jama’a ta hanyoyi masu munin gaske.”