✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta karbo bashin $1bn saboda matsalar rashin ayyukan yi

Gwamnatin Tarayya ta karbo wani sabon bashi na Dala biliyan daya domin inganta kanana da matsakaitan masana’antu a fafutikar da take yi na magance matsalar…

Gwamnatin Tarayya ta karbo wani sabon bashi na Dala biliyan daya domin inganta kanana da matsakaitan masana’antu a fafutikar da take yi na magance matsalar rashin ayyukan yi a Najeriya da kuma mikar da komadar tattalin arziki.

An karbo bashin ne ta hannun Bankin Masa’anantu karkashin Ma’aikatar Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Hannun Jari ta kasa.

Ministan Ma’aikatar, Otunba Adeniyi Adebayo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani shiri na karfafa wa kanana da matsakaitan masana’antu da aka gudanar a Kamfanin Quantum Mechanics da ke Abuja.

Ministan ta bakin mai magana da yawunsa, Ifedayo Sayo, ya ce bashin zai taimaka wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i da nufin karfa tattalin arzikin kasar.

A cewar Mista Sayo, wannan wani mataki ne na tayar da komadar tattalin arzikin kasar da kuma tabbatar da cewa ya ci gaba da dorewa.