✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a dauki tsoffin ‘yan N-Power aikin gwamnati

Ministar Agaji da Kyautata Rayuwa Sadiya Umar Farouq ta ce Gwamantin Tarayya na shirin daukar wadanda aka yaye a shirin tallafi na N-Power aiki. Sadiya…

Ministar Agaji da Kyautata Rayuwa Sadiya Umar Farouq ta ce Gwamantin Tarayya na shirin daukar wadanda aka yaye a shirin tallafi na N-Power aiki.

Sadiya ta bukaci matasan da su kara haukuri kafin fitowar sakamakon kokarin da ake yi na ganin yadda za a shigar da wadanda suka cancanta daga cikinsu aikin gwamnati.

“Mun umarci masu kuda da Shirin Tallafa wa Matasa a Jihohi da su gabatar mana da cikakken jerin sunayen tsoffin ‘yan N-Power da ke sha’awar shiga shirin”.

Sanarwar ta mai ba ta shawara kan yada labarai, Misis Nneka Anibeze, ta kara da cewa, “An ba da izinin biyan alawus din da rukunin farko da na biyu da suka kammala shirin suke bin bashi”.

“An riga a gabatar wa Ofishin Akanta Janar ta Tarayya umarnin biyan alawus din watan Yunin 2020 ga rukunin domin ya kara dubawa ya biya su.

“Abin da kawai ya rage a mika wa Ofishin shi ne na biyan alawus din rukuni na biyu na watan Yuli”, inji sanarwar.