✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta gina gidaje 1,000 a jihohin Arewa 7 — Shettima

Wannan na daga cikin wani yunkuri na rage raɗaɗin waɗanda rikici ya shafa a yankin.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya ce Gwamnatin Tarayya za ta gina gidaje 1,000 a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya shida da kuma Benuwe.

Shettima ya ce wannan na daga cikin wani yunkuri na rage raɗaɗin waɗanda rikici ya shafa a yankin.

A cewarsa, jihohin sun haɗa da Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Neja sai kuma Benuwe.

Shettima ya bayyana hakan ne a Borno, lokacin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu yayin buɗe wasu ayyuka 77 da Gwamna Babagana Umara Zulum ya aiwatar a cikin kwanaki 100 na farkon wannan wa’adi na biyu na gwamnatinsa.

Wasu daga cikin ayyukan da Shettima ya buɗe akwai makarantar Shuwari da wata cibiyar lafiya, akwai makarantar Alikaramti da ta Gamboru dukkansu a cikin garin Maiduguri.

Mataimakin ya bayyana cewa gidaje 1,000 da shugaba Tinubu ya amince da su, za a gina su ne da duk wasu kayayyakin more rayuwa kama daga makarantu, dakunan shan magani, asibitocin dabbobi da wuraren kiwo na fulani makiyaya.