Gwamnatin Filato ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar | Aminiya

Gwamnatin Filato ta soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar

Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong
    Ado Abubakar Musa, Jos da Abubakar Muhammad Usman

Gwamnatin Jihar Filato ta soke lasisin dukkan makarantun Firamare da Sakandare masu zaman kansu da ke fadin jihar.

Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Elizabeth Wampum, ce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Jos, babban birnin jihar ranar Alhamis.

A cewar kwamishiniyar, an dauki matakin ne bayan gano cewa sama da makarantu masu zaman kansu 5,000 ne ke gudanar da ayyukansu ba tare da lasisi ba.

Ta ce kaso 90 cikin 100 na makarantu masu zaman kansu a Filato ba sa bin ka’idojin gwamnati, inda ta ce kaso 85 na makarantun masu zaman kansu 495 da aka bai wa lasisi a baya ba sa bai wa gwamnatin hadin kai.

Elizabeth ta ce, “Muna amfani da wannan dama don sanar da jama’a cewa an kwace lasisin duk makarantun Firamare da Sakandare masu zaman kansu da ke jihar nan, an bukaci su sake sabunta takardun shaidarsu.”

Sai dai kwamishiniyar ta ce an aiwatar da matakin ne domin duba yawaitar makarantu masu zaman kansu da ba su dace ba da kuma tallafa wa wadanda ke gudanar da aiki bisa tsarin doka, domin a samu ilimi mai inganci ga kowa da kowa.