✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

Gwamnatin Gombe ta haramta wa manoma kona daji bayan kwashe amfanin gona

Gwamnatin ta ce dole a bar wa makiyaya karmami su kalata

Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da dokar haramta wa kananan yara kiwo da kona daji da wasu manoma ke yi bayan kwashe amfanin gonarsu.

Kwamishinan Gona da Gandun Daji na jihar, Muhammad Magaji Gettado, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyana wa manema labarai sakamakon zaman Majalisar Zartarwar Jihar karo na 26.

Ya ce saboda matsaloli na karancin abinci da za a iya fuskanta na ta’adin dabbobi, gwamnatin ta haramta wa manoma yin kaura su shigo jihar ko su bar ta wasu jihohi da kuma tsakanin Karamar Hukuma zuwa wata.

Kwamishinan ya kuma ce Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce doka ne a kama kananan yara suna kiwo, ko kuma masu kiwon dare.

A cewarsa dokar ta fara aiki nan take har zuwa karshen watan Janairu, kuma duk wanda aka kama ya karya dokar zai dandana kudarsa.

“Duk manomin da ya kwashe amfanin gonarsa ba a yarda ya kona karmamin da ya rage ba saboda idan kowa ya kammala kwashe amfanin gonar ya bar wa makiyaya su kalaci abin da za su ci,” inji shi.