✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta yi raddi kan kalaman Jafar Jafar

Gwamnatin ta ce Jafar Jafar ya yi wa kalaman Ganduje gurguwar fahimta.

Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani kan kalaman Jafar Jafar na cewar duk abin da ya same shi a tuhumin Gwamna  Abdullahi Ganduje.

Gwamnatin ta yi raddin ne ta bakin Kwamishinan Yada Labaranta, Muhammad Garba, inda ya ce dan jaridar ya yi wa kalaman gwamnan gurguwar fahimta.

“Yanzu haka maganar na gaban kotu, don haka sai a jira a ga abin da zai biyo baya.

“Kalaman gwamnan na nufin zai ci gaba da daukar matakan shari’a ba wai nufin yi masa wani abu ba,” a cewar Garba.

Ganduje, ya ce za su yi maganin wanda suka shirya bidiyon karbar ‘Dala’ a yayin tattaunawa da aka yi da shi a a shirin ‘A Fada A Cika’ na Sashen Hausa na BBC, kalaman da ya bar baya da kura.

Hakan ya sa Jafar Jafar, mai jaridar Daily Nigerian yin karar Gwamnan Kano gaban Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, cewa gwamnan na barazana ga rayuwarsa.

Tun shekarar 2018 ne Jafar Jafar ya saki wani bidiyo, wanda a ciki aka ga gwamnan na karbar bandur-bandur na ‘Dala’, yana sanyawa a aljihun babbar rigarsa.

Hakan ya tada yamutsi a Jihar Kano da ma Najeriya, inda ake zargin gwamnan da karbar cin hanci a wajen ’yan kwangila kafin ba su aiki.

A dalilin haka ya sa EFCC ta bincike bidiyon kuma ta tabbatar da sahihancinsa.

Sai dai lamarin na gaban kotu, inda Gwamnatin Kano ta shigar da Jafar Jafar kara kan zargin bata wa gwamnan suna.