✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano za ta kirkiro hukumar yaki da bara

Gwamnatin Kano ta sha alwashin yaki da bara a kan titunan jihar.

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar yaki da bara a fadin jihar ta hanyar hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu, don yakar dabi’ar bara da ke neman zama barazana.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, yayin da yake karbar bakuncin shugabannin gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu a fadar gwamnatin jihar a ranar Talata.

Gamayyar kungiyoyin masu zaman kansu karkashin jagorancin Malam Ibrahim Waiya, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tsaurara matakai wajen yakar barace-barace a kan titunan jihar.

Gwamna Ganduje ya shaida wa kungiyoyin cewa za a kafa hukumar tare da samar mata da ma’aikatan da za su yi aiki tukuru wajen yakar dabi’ar bara a jihar.

“Ba za mu zura ido muna gani ana lalata rayuwar kananan yara ta hanyar barace-barace a kan tituna ba,” a cewar gwamnan.

Ya kara da cewar barace-barace da yara ke yi na daga cikin hanyoyin da ake cutar da su, wanda hakan na hana su samun ilimin addini dana zamani.

Kazalika, gwamnan ya nuna jin dadinsa kan yadda kungiyoyin suka nuna damuwarsu kan lamarin, inda ya ba su tabbacin za a yi tafiya da su don tabbar da samun nasara.

“Mun yi farin ciki da zuwanku kuma muna godiya kan yadda kuka nuna damuwarku.

“Tabbas, wannan lamari ne da ya kamata a tashi tsaye a kansa, dole mu fito da hanyoyin magance wannan matsala,” kamar yadda ya bayyana.

Tun farko, kungiyoyin sun aike wa da gwamnatin jihar da takarda, inda suka bukaci ta ayyana dokar hana yin bara a kan titunan fadin jihar.

Gwamnan Jihar, ya bayyana musu cewa Gwamnatin Jihar Kano ta karbi takardar kuma za ta yi duba tare da dabbaka abin da ya dace a kai.