✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kebbi ta tube rawanin Hakimin Sauwa

Gwamnatin ta kama hakiman biyu da laifin rashin yi mata biyayya.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tube rawanin Hakimin Sauwa, Alhaji Muhammad Tajudden-Sauwa, bisa laifin rashin yi mata biyayya.

Kazalika, gwamnatin ta dakatar da Hakimin Guluma na tsawon wata shida, Alhaji Muhammad Bashir-Guluma.

Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kebbi, Alhaji Ahmed Idris ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, a ranar Asabar.

Idris, ya ce kwamitin da hukumar kula da ma’aikata ta Karamar Hukumar, ta kafa a ranar 31 ga watan Janairu, ta samu masu sarautun gargajiyar biyu da laifin rashin yin biyayya ga gwamnatin jihar.

An kafa kwamitin ne biyo bayan korarin da shugaban Karamar Hukumar Arugungu ya kai na hakiman biyu.

Ya ce kwamitin ya bayar da shawarar mataki karkashin dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 030301(0), wadda ta shafi rashin yin biyayya.

Idris, ya ce hukuncin dakatar da hakiman biyu za ta fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Fabrairu, 2024.