✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita ranakun hutun sallah

Majalisar Ƙolin Musulunci ta Nijeriya ta ayyana Laraba a matsayin ranar bikin sallah.

Gwamnatin Tarayya ta amince da sanya Alhamis, 11 ga watan Afrilun 2024 a cikin jerin kwanakin hutun karamar sallah da ta bayar.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dokta Olubunmi Tunji-Ojo ya fitar a safiyar wannan Talatar.

Wannan na zuwa ne sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a jiya Litinin da zai kawo ƙarshen watan Ramadan.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariya a Ma’ikatar Harkokin Cikin Gida, Dokta Aishetu Gogo Ndayako, tana kuma taya al’ummar Musulmi kammala Azumin watan Ramadana lafiya tare da fatan Allah Ya karɓi ibadu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta ayyana wannan Talatar da gobe Laraba a matsayin ranakun hutun sallah karama a faɗin Najeriya.

Sai dai kuma a sakamakon rashin ganin watan Shawwal ne Majalisar Ƙolin Musulunci ta Nijeriya ta ayyana Laraba a matsayin ranar bikin sallah.

Gwamnatin Tarayya dai ta saba bayar da kwanaki biyu ne a matsayin ranakun hutun sallah domin ma’aikata da sauran al’ummar ƙasar.