✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni sun munafunce ni —El-Rufai

El-Rufai ya zargi wani gwamna da ba NLC kudade domin su tsayar da harkoki a Jihar Kaduna.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya caccaki Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kan abin da ya kira munafuntarsa da suka yi a lokacin yajin aikin da Kungiyar Kwadago ta NLC ta yi a jiharsa.

A lokacin zaman gwamnonin na ranar Laraba, El-Rufai ya zargi kungiyar da zama bakin ganga a yayin da jayin aikin ya tsayar da harkoki a jiharsa na tsawon kwanaki.

“Ni gwamna ne kuma daya ne daga cikinku. Na yi tsammanin akalla Kungiyar Gwamnonin Najeriya za ta fito karara ta mara mini baya. Amma hakan ya gagara.

“Ba zan yi boye-boye be. Zan iya nuna muku cewa babu komai har in yi murmushi in ce komai na tafiya yadda ya kamata, amma ba ni haka ba ne. Ni na saba tunakarar matsalolina na kadai,” inji El-Rufai.

El-Rufai ya yi zargin cewa wani gwamna ne ya taimaka wa NLC da kudade domin ta tayar da zaune tsaye a Jihar Kaduna.

NLC ta yi yajin aikin gargadi da zanga-zangar lumana kan sallamar ma’aikata 45,000 da gwamnan ya sallama ‘ba bisa ka’ida ba’.

Lamarin ya kai ga kungiyoyin da ke karkashin inuwar NLC sun fara shirin shiga yajin aiki na gama-gari a fadin Najeriya, kafin Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani domin sasanta bangarorin.