✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Hadarin mota ya kashe mutum 3 a Kano

Nan da nan gobara ta cinye motar bas din.

Mutum uku ne aka samu labarin mutuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata a sakamakon wani hadarin mota da ya afku a Karamar Hukumar Takai ta Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Saminu Yusuf Abdullahi a ranar Lahadi.

Ya ce, hadarin ya hada da wata mota kirar Toyota Hilux mai dauke da mutum uku da suka taso daga Jihar Jigawa da wata motar fasinja kirar bus mai dauke da fasinjoji 15 da suka taso daga Kano.

A cewarsa, nan take bayan da motocin suka yi karo, motar bus din kirar hummer ta kama da wuta inda aka yi nasarar ceto mutum uku a sume, yayin da sauran wadanda abin ya rutsa da su suka samu raunuka.

“Bayan samun labarin, cikin gaggawa muka aika jami’anmu zuwa wurin da hadarin ya afku domin kai dauki.

“Da isowarmu, sai muka tarar wata motar bas ce ta haya kirar Hummer marar lambar rajista mai dauke da fasinjoji 15 da suka taso daga Kano.

“Motar dai ta yi karo da wata mota kirar Toyota Hilux dauke da mutum uku da suka taho daga Jigawa

“Nan da nan gobara ta cinye motar bas din.