✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haduwar Daliban Afaka da iyayensu cikin hotuna

Farin cikin iyaye da daliban a lokacin haduwarsu ranar Juma'a.

A ranar Juma’a daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da aka yi garkuwa da su suka koma hannun iyayensu.

Ragowar daliban su 27 da aka sako sun shafe kusan wata biyu a hannun ’yan bindigar.

Ga hotunan yadda haduwarsu da iyayen nasu ta kasance a harabar kwalejin.

Uwa da da! Dattijuwar nan cikin farin ciki ta goya ‘yarta bayan haduwarsu. (Hoto: Lami Sadiq).
Mahaifiyar daya daga cikin daliban rungume da shi cikin farin ciki bayan haduwarsu a ranar Juma’a. (Hoto: Lami Sadiq).
‘Yan uwan dalibar nan sun zagaye ta, wanta ya dora ta a kafada. Ana ta daukar su hoto. Dan uwa rabin jiki! (Hoto: Lami Sadiq).
Iyayenta sun rungume ta za su tafi gida. Sama da wata biyu rabonsu da yin ido hudu da juna. (Hoto: Lami Sadiq).
Lokacin tarihi! Iyayen wani daga cikin daliban, suna daukar hoto bayan ya dawo wurinsu. (Hoto: Lami Sadiq).
Wata dalibar da aka sako tana zubar da hawayen farin cikin haduwarta da mahaifinta. (Hoto: Lami Sadiq).
Bayan saukar daliban daga motocin da suka kawo su Kwalejin washegarin ranar da suka iso Kaduna. (Hoto: Lami Sadiq).
Kukan zuci bayan haduwar wannan mahaifiya da ‘yarta. (Hoto: Lami Sadiq).
Daliban a lokacin da suke dab da komawa ga iyayensu. (Hoto: Lami Sadiq).
Wani sashe na daliban da aka sako. (Hoto: Lami Sadiq).