✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Fatima Ibrahim Shema: Hakuri sirrin nasarar rayuwa

Kada mata su raina sana’aHajiya Fatima Ibrahim Shehu Shema ita ce uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema. A hirar da ta yi da…

Hajiya Fatima Ibrahim ShemaKada mata su raina sana’a
Hajiya Fatima Ibrahim Shehu Shema ita ce uwargidan Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema. A hirar da ta yi da Zinariya ta ce hakuri shi ne sirrin nasarar rayuwar aure. Ta ce kada mata su raina jari komai kankantarsa kasancewar ita ma ta fara kasuwanci da karamin jari ne.
Tarihin rayuwata
An haife ni a garin Zariya.  Na taso tare da ‘yan uwana takwas maza da mata. Na yi Makarantar Firamare ta Jafaru da ke Zariya, sannan da na gama sai na tafi GGSS Kawo. Daga nan sai na je Kwalejin Share fagen shiga Jami’a ta Katsina wacce ke Zariya (CAR). Bayan na kammala sai na samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, inda na karanta kasuwanci (Business administration) Bayan na kammala digirina sai na yi hidimar kasa a Zariya. Bayan hidimar kasa sai na yi aure. Duk da cewa ban taba yin aikin gwamnati ba, ban zauna haka kawai ba sai na kama harkar kasuwanci gadan-gadan.
Iyalina
Mun hadu da maigidana Malam Ibrahim Shehu Shema tun muna Makarantar CAS. Bayan na gama hidimar kasa Allah Ya nufa muka yi aure. Allah Ya albarkace mu da ‘ya’ya hudu, maza uku da mace daya.
Ayyukana
Tun daga lokacin da Allah Ya nufi maigidana da samun mulkin wannan jiha nake ta tunanin abin da zan yi domin daga darajar matan wannan jiha don su amfana. Hakan ya sa muka fito da shirinmu na “Serbice to Humanity ‘ inda muke aikace-aikace da dama don kyautata tare da inganta rayuwar mata da kananan yara a Jihar Katsina. A yanzu haka mun samar wa mata ayyukan yi ta yadda za su rika samun dan dari da kobo. Haka kuma muna shirya musu bita don ganin sun sami wayewa a kan rayuwarsu da ta iyalansu.
 Game da abin da ya shafi ci gaban kananan yara ma muna kokarin nuna wa iyaye muhimmancin kula da ‘ya’ya, musamman game da abin da ya shafi almajirci. Muna nuna wa matan karkara cewa su daina yarda ana kai ’ya’yansu birane da niyyar yin karatu. Idan aka duba a ko’ina akwai makarantun Islamiyya, don haka su rika barin ‘ya’yansu suna karatu a kusa da su. Haka kuma abin da ya shafi batun kula da abincin iyalansu muna kokari game da nuna wa matan nan muhimmancin cin abinci mai gina jiki ba wai sai mai tsada ba, muna da cimaka tamu ta gargajiya wadanda ke kewaye da mu irinsu zogale da sauransu. Haka kuma game da abin da ya shafi kula da lafiyarsu misali irin cututtukan da suka shafi skill sel da sauransu muna wayar musu da kai cewa ana iya kauce wa kamuwa da cutar ta hanyar yin gwajin jini kafin yin aure da sauransu.
Ta bangaren samar musu da abin yi a kowane wata gwamnati na ware wasu kudi da ake raba wa mata a jihar, inda ake ba mata dari Naira dubu goma-goma a kowace karamar hukuma da ke jihar, don su samu abin da za su yi jari da shi. Baya ga wannan kuma a kwanan nan muka kaddamar da wani shiri na kara karfafa wa mata sana’o’insu, inda muka shiga kananan hukumomi 34 na jihar muka zabo mata 1500 muka tallafa musu da jarin da za su kara bunkasa sana’arsu, misali matan da ke kosai muka ba wa kowacce buhun wake daya da jarkar mai daya da tsabar kudi Naira dubu 10. Wadanda ke sana’ar awara kuma muka ba su buhun waken suya da mai da Naira dubu goma, haka su ma wadanda ke yin sana’ar da ta shafi fulawa muka ba su buhun fulawa da mai da Naira dubu 10.

A game da haka mun yi shiri sosai wajen ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, yadda matan za su rika amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace. Abin da muka yi shi ne sai muka hada kai da kungiyar WOFAN inda za su rika taimaka mana ta hanyar bin matan nan a wuraren sana’o’insu suna bibiyar abubuwan da suke gudanarwa tare da ba su shawarwarin yadda za su habaka sanao’insu. Kamar a kwanakin baya da muka raba gyada da injinan markade da na matsar gyada da kuma kudi Naira dubu 50 ga matan kowace karamar hukuma a jihar nan, wanann kungiya ta WOFAN ita ke bi ta tabbatar an kafa wadannan injina tare da yin amfani da su yadda ya kamata, kai ita ce kan gano ko akwai matsala da yadda za a magance ta.
Burina a rayuwa
Burina a rayuwa shi ne na taimaki jama’a. A rayuwa ba wai abin da mutum ya ci ko ya daura shi ne nasa ba. Kamar yadda ake gaya mana cewa idan ka taimaka wa wani ya yi farin ciki ya samu natsuwa wannan shi ne ribarka a rayuwa.
Abin koyi
Zan iya cewa wacce ta zama abar kwaikwayo a wurina ita ce mahaifiyata. Kasancewar mahaifina ya rasu tun ina karama lokacin da zan shiga makarantar sakandire, don haka mahaifiyarmu ita ta tsaya tsayin daka a kanmu, musamman abin da ya shafi karatunmu har muka kammala. Dukkaninmu mu takwas din nan babu wanda bai yi digiri ba. Mun san ciwon kanmu mun samu tarbiyya yadda za mu girmama na gaba da sauransu. Babu shakka mahaifiyata ita ce abar koyi a wurina saboda mace ce tsayayyiya, kuma jajirtacciya.
Abin da take so mutane su tuna ta da shi
Ina so wata rana mutane su tuna cewa akwai wata Fatima Shema da ta taba zama a wurin nan ta taimake su har ma suka sami natsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsu. A takaice ina so a tuna ni a matsayin wacce ta taimaki rayuwar jama’a.
Shawararta ga mata
Ina shawartar ‘yan uwana mata da kada su raina jari komai kankantarsa, a yi kokarin ririta shi har wata rana a kai ga samun babban jari. Ni ma kaina kamar yadda na bayyana a baya na yi sana’oi iri daban-daban; lokacin da na fara harkar kiwo da kadan na fara inda nake zuba kaji 20 zuwa 50, a hankali wata rana sai ga shi na kai ina zuba dubbai. Saboda haka mata kada a yi wasa da sana’a kowacce iri ce a damke ta da kyau.
Game da abin da ya shafi zamantakewr iyali ma, a wannan bangare kuma hakuri ne sirrin nasarar rayuwar aure. Idan aka sanya hakuri a cikin komai  aka kuma sanya Allah a gaba za a samu cin nasara insha Allah. A yi ta hakuri da juna. Zaman hakuri shi ke kawo ci gaba a rayuwar zamantakewa. Idan aka yi hakuri, to insha Allahu sai abubuwa su zo mana da sauki.
Haka kuma mata akwai bukatar mu kula da ‘ya’yanmu da kyau, mu san cewa  ‘ya’yanmu amanar Allah  ce a hannunmu. Yadda rayuwar yau ta zama ta guje-gujen neman abin duniya, akwai bukatar mu rika samun natsuwa muna  kula da tarbiyyar ’ya’yanmu. A nan ne za mu nuna musu abin da ya kamata da wanda bai kamata ba don rayuwarsu ta inganta.
Abin da na fi sha’awa
Ina da sha’awar yin girke-girke, duk da cewar a yanzu ba na samun cikakken lokaci na yi girkin. Haka kuma ina sha’awar kiwon dabbobi. Har ila yau kuma ina son yin tafiye-tafiye. Haka kuma ina son hawa tsauni, don haka nake son duk wani wuri da ke da wannan abubuwa.
Kwalliya
Ni ba mace ba ce mai bin yayin kwalliya. Ina daukar duk abin da ya kwanta min a rai na yi amfani da shi. Sai a yi yayin abu na kwalliya a gama ban san ma an yi ba.
Abincin da na fi so
To kin san bazazzagiya ce ni don haka ba abincin da na fi so a rayuwa irin fate. Haka kuma ina son ‘ya’yan itace, don da ka hana ni ‘ya’yan itatuwa gara ka hana ni abinci.