✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji: 15 ga watan Mayu za a fara jigilar maniyyata

Maniyyata kimanin 65,000 ne za su sauke farali daga Najeriya, inda ake sa ran za su yi akalla kwana hudu a Madina domin yin Ziyara,…

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar cewa ranar 15 ga watan nan na Mayu za a fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya.

Shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, ne ya sanar da haka a taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah da ke gudana a Abuja a safiyar Alhamis.

Jalal Arabi ya ce a bana maniyyata kimanin 65,500 ne za sauke farali daga Najeriya, inda za su shafe akalla kwanaki hudu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a y jigilar maniyyata ne daga cibiyoyi 10 a fadin Najeriya.