✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2023: An ba wa jihohi kujerun maniyyata 75,000

Za a ba wa maniyyatan wasu kasashe gadaje masu hawa biyu

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta ware wa maniyyatan  jihohi da Babban Birnin Tarayya kujerun 75,000 domin sauke farali a bana.

Mataimakin Daraktan Yada Labaran NAHCON, Mousa Ubandawaki, ya ce ragowar kujeru 20,000 da suka rage kuma an ba wa maniyyata masu bin jirgin yawo.

Ya ce an tsara haka ne a lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar aikin Hajjin 2023 tsakanin NAHCON da Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya, wadda ta ba Najeriya kujerun alhazai 95,000.

“Wakilan Najeriya daga NAHCON sun ganada da Shugaban Mutawwif na kasashen Afirka da ba Larawa ba, Ahmad Sindi, kuma ya ba da tabbacin cewa aikin Hajjin 2023 zai fi na bara inganta,” in ji Ubandawaki.

Ahmad Sindi ya ce bana za a ba wa maniyyatan wasu kasashe gadaje masu hawa biyu, da nufin samar musu karin dakuna da sarari a ranakun aikin Hajji.

Don haka a bukaci kasashe da su ba da hadin kan da ake bukata don ganin an yi aikin Hajjin bana cikin nasara.