✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajji 2024: Kamfanonin jirgin yawo 40 za su yi jigilan maniyyatan Najeriya

Kasar Saudiyya ta kara yawan kamfononin jirgin yawo da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya a aikin Hajjin 2024 zuwa 40 daga 10.

Kasar Saudiyya ta kara yawan kamfanonin jirgin yawo da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya a aikin Hajjin 2024 zuwa 40 daga 10.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce sassaucin da Saudiyya ta yi zai kara saurakaka wa Najeriya jigilar maniyyatan kasar.

Da farko NAHCOn ta tantance kamfanonin jirgin yawo 110 domin jigilar maniyyatan Najeriya a 2024.

Sai dai Ma’aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta kayyade kashi 5% na kamfanonin jirgin yawo na kasashe masu alhazai damar jigilar.

Da haka ne Najeriya ta kare da samun kamfanoni 10, kafin Saudiyyar ta sassauta gabanin aikin Hajjin 2024 da ke tafe.

Sanarwar NAHCON ta ce kamfanonin jirgin yawo 40 da suka fi samun maki daga cikin 110 da ta tantance ne za su yi aikin a bana.

Ta kara da ragowar 70 din da da su hada kai da 40 din da aka zaba wajen gudanar da aikin cikin nasara.