Hanifa: Budurwar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a kotu | Aminiya

Hanifa: Budurwar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a kotu

Abdulmalik Tanko da Hanifa, yarinyar da ake tuhumarsa da kashewa a Kano
Abdulmalik Tanko da Hanifa, yarinyar da ake tuhumarsa da kashewa a Kano
    Lubabatu I. Garba, Kano

Fatima Jibril, budurwar Abdulmalik Tanko, mutumin da ake zargi da kisan dalibarsa Hanifa Abubakar, ta bayyana yadda ya yaudare ta da alkawarin aure ya sa su sace yarinyar a makarantar Islamiyya.

Fatima ta bayyana bayan an gurfanar da ita tare da wani mai shuna Hashim Isyaku a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako karkashin jagorancin Mai sharia Usman Naabba domin bayar da shaidar kariya.

A jawabansu daban-daban game da kisan Hanifa mai shekara biyar, mutanen sun bayyana cewa Abdulmalik ya yaudare su ne har ya kai ga sanya su a cikin kes din.

Fatima, mai kimanin shekara 25 da ke sana’ar sayar da kayan miya, ta shaida wa kotu cewa Abdulmalik ya yaudare ta ya shigar da ita kes din garkuwa da Hanifa ne da alkawarin cewa zai aure ta da kuam saya mata kayan daki.

A cewarta, tun daga lokacin da suka yi kokarin sace Hanifa a makarantar Islamiyya amma abin bai yiwu ba, ba ta sake haduwa da Abdulmalik ba sai lokacin da aka kama shi aka zo aka tafi tare da ita.

A nasa bangaren, Hashim Isyaku, mai kimanin shekara 37 ya ce Abdulmalik ya shaida mishi cewa akwai wata mata da mijinta ke son karin aure don haka take so a yi garkuwa da ’yarta domin mijin nata ya manta da batun auren.

“Sai ya dauko wayarsa ya nuna min hoton yarinyar inda ni kuma na gaya mishi cewa yin hakan laifi ne amma sai ya gaya min cewa babar yarinyar ce ta shirya hakan da kanta don haka babu komai.

“Washegari dai ya zo gidana ya dauke ni a Keke NAPEP don gudanar da aikin daukar yarinyar inda ya kai ni wani waje ya ajiye ni tare da ba ni lanmbar wayar wata mata da ya ce za mu yi aikin daukar yarinyar tare.

“Bayan mun hadu da Fatima a Kwanar Dakata inda muka tsaya don fitowar yarinyar daga makaranta.

“Bayan yara da yawa sun wuce sannan muka ga yarinyar da za mu dauka ta zo wurin inda muka yi kokarin daukar ta amma abin bai yiwu ba. Daga nan ne muka koma gida.”

A cewar Hashim tun daga wannan lokaci ba su kara haduwa da Abdulmalik ba sai ranar da ya kira shi domin ya zo ya binne masa dan tayin da matar makwabcinsa ta yi barinshi, wanda a cewarsa makwabcin nasa ba ya gari.

Alkalin kotun, Mai sharia Usman Naabba ya dage zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Yuni, 2022.