✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi 9 da rashin samun isasshen barci ke cutar da dan Adam

Aminiya ta tattaro wasu hanyoyi guda tara da rashin samun isasshen barci ke cutar da dan Adam.

Rashin samun wadataccen barci na da matukar illa ga lafiyar dan Adam. Mutane da dama kan fuskanci matsalar ne idan suka kasa yin barci kwata-kwata, ko suka gaza yin barcin a cikin sauki, musamman in hakan na faruwa akalla sau uku a mako, na sama da wata uku. Akwai bukatar a gaggauta ganin likita da zarar an fuskanci wannnan matsalar. Rashin samun barci na tsawon lokaci dai na iya haifar da gagarumar matsala ga lafiyar dan Adam.

Ga wasu hanyoyi guda tara da rashin samun isasshen barci ka iya cutar da dan Adam

Yawan kasala

Matsalar na faruwa ne idan mutum a kodayaushe jikinsa na ksancewa cikin kasala, lamarin da kan kai ga shafar ayyukan mutum na yau da kullum.

Kasala na daya daga cikin manyan alamomin rashin barci. Wani lokacin matsalar na iya haifar da matsanancin ciwon kai, yawan jin barci da kuma rikewar gabobi.

Rashin walwala

Rashin samun barci na tsawon lokai na iya jefa mutum a yanayin yawan bacin rai, tare da sanya mutum kullum ya kasance cikin rashin walwala.

Idan matsalar ta dada ta’azzara, za ta iya haifar da matsaloli irinsu matsananciyar damuwa. Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa masu fama da karancin barci na da barazanar kamuwa da cutar bacin rai har sau biyar fiye wadanda ba su da matsalar.

Yawan gajiya

Mutanen da suka manyanta amma ba sa samun barci akalla na sa’a takwas a kullum za su iya fuskantar yawan gajiya, ko ransu ya rika saurin baci, fiye da wadanda suke barci sosai, kamar yadda wani bincike na Kungiyar Masana Halayyar dan Adam ta Amurka (APA) ya gano.

Yawan mantuwa

Idan mutum ya dauki tsawon lokaci yana samun karancin barci, akwai yiwuwar ya haifar masa da yawan mantuwa, rashin mayar da hankali akan abubuwa da kuma rashin iya yanke shawara.

Karuwar kiba

Kazalika, rashin samun isasshen barci na akalla sa’a bakwai a kullum ka iya haifar da karuwar kiba. Masana ilimin Kimiyya sun gano cewa hakan na faruwa ne sakamakon yadda rashin baccin ke shafar sinadaran hormones, wadanda sune ke samar da yanayin jin yunwa da kuma koshi.

Rashin samun barcin na wasu tsawon lokuta na iya jefa mutum cikin barazanar kamuwa da mummunar kiba da kuma sauran cututtuka masu alaka da ita kamar ciwon suga, hawan jini da kuma ciwon zuciya.

Raunin garkuwar jiki

Lokacin da mutum yake barci, jikinsa kan fitar da sinadaran da suke kare shi daga kamuwa da cututtuka. Matsanancin rashin barci na iya shafar hakan, ta hanyar rage yawan sinadaran da ke taimaka wa jiki yaki da cututtuka.

Bincike ya nuna cewa mutanen da ba sa samun isasshen barci sun fi barazanar kamuwa da kwayoyin cuta kamar su sanyi da mura, idan suka kusanci masu dauke da su.

Ciwon suga

Daya daga cikin cututtukan da mara samun isasshen barci zai iya kamuwa da su ita ce cutar ciwon suga sakamakon yadda matsalar ke shafar yadda jiki ke sarrafa suga.

Ciwon zuciya

Karancin barci na kuma iya shafar zuciya da yadda take aiki. Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa rashin barci ko da na kwana daya ne na kawo karuwar matsalar jini ga mutumin da ya manyanta.

Idan matsalar ta ci gaba da faruwa tsawon lokaci, za ta iya sa zuciyar ta rika tunkudo jini fiye da kima ga jiki, wanda zai iya sa wa ta sami matsala.

Karuwar barazanar yin hatsari

Yiwuwar barazanar samun hatsari na iya karuwa in aka shafe tsawon lokaci ba a samun isasshen barci. Hakan na faruwa ne saboda matsalar gyangyadi da kuma rashin mayar da hankali akan abin da mutum yake yi.

A wani bincike da aka yi akan direbobin manyan motoci sama da 900, an gano cewa marasa samun wadataccen barci na cikin barazanar yin hatsari fiye da wadanda suke yi.