✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu gas din girki na gagarar talaka bayan wata daya da alkawarin gwamnati

A hakan ma an samu rangwame saboda tsoma baki da Tinubu ya yi.

A halin yanzu wata guda ke nan bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin karya farashin iskar gas din girki, a yayin da magidanta da ‘yan kasuwa ke ci gaba da biyan farashi mai tsada kan kowane kilogiram daya na gas din.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da farashin gas din ya tsaya cak sai ma hawa da yake yi, inda binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa ba a samu wani sauyi ta fuskar rahusa da zai kawo sauki a lamarin ba.

Ana iya tuna cewa a bara ne Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman don bibiyar yadda farashin iskar gas ta girki ke ci gaba da tashin gwauron zabi a sassan kasar.

Wata sanarwa da ma’aikatar makamashi ta kasar ta fitar a ranar 26 ga watan Nuwamban bara, ta ruwaito Minista Ekperikpe Ekpo na bayyana matukar damuwa da yadda farashin na gas ke ci gaba da tashi a sassan kasar.

Ministan a wancan lokaci ya ce cikin kasa da mako guda kwamitin da aka dorawa alhakin warware matsalar zai shawo kan tsadar iskar ta gas da kuma aikin rarraba shi zuwa sassan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun a watan Nuwamban na bara farashin gas din na girki ya haura naira 1,200 kan duk kilogiram, inda ko a a shekarar da ta gabata Kungiyar Masu Sayar da Gas din Girki ta Najeriya (NALPGAM), ta ce ci gaba da faduwar darajar Naira na iya sa farashin gas ya tashi a kasar nan da mako mai zuwa.

Haka kuma, da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Najeriya (NAN) a Agustan bara, Shugaban NALPGAM, Olatunbosun Oladapo ya yi gargadin cewa a ’yan kwanakin nan, manyan dillalan gas din sun bayyana cewa farashinsa ya karu, inda ya alakanta hakan da faduwar darajar Naira.

Oladapo ya kuma ce karuwar farashin gas din a kasuwar duniya da karin haraji da karancin canjin kudi da kuma karya darajar Naira na daga cikin dalilan da za su sa farashin ya karu.

“Akwai yuwuwar ya tashi nan da mako mai zuwa saboda farashinsa ya tashi a kasuwar duniya. Dukkan dillalai da masu sayarwa kadan-kadan da kuma ’yan sari duk yanzu suna fama da kalubale.

A wasu sassa na Najeriyar bayanai sun ce ana sayar da duk kilo guda kan farashin fiye da naira dubu 1 da 100.

‘Yanzu gas din girki ya gagare mu’

Wata matar aure mai suna Catherine Joseph da ke zaune a unguwar Sabon Gari a Kano, ta ce gas din girki ya fi karfinta a yanzu.

“Idan za ku dafa wa iyali mai mutum biyar abinci sau uku a rana, kilo 12 na iskar gas, wanda a yanzu ya haura N11,000 ba zai wuce wata daya ba.

“Kuma idan aka dubi lissafin kasafin kuɗin da muka yi na wata daya da kyau, ba zai yiwu mai matsakaicin samu ya iya sayen gas din ba.

“Yanzu mun hakura mun koma amfani da gawayi da itace duk da cewa su ma ba a barsu ba wajen tsada,” inji ta.

Mardiyya Sabiu, wata mai sayar da abinci a Kano ita ma ta ce lamarin sana’arta ya shiga tsilla-tsilla ne tun lokacin da aka kara farashin man fetur sannan kuma farashin iskar gas ma ya tashi.

“An gaya mana cewa gas ne zai fi kawo mana sauƙi a madadin man fetur amma da alama har yanzu muna cikin matsala tun bayan cire tallafin man fetur, wanda kuma ya shafi farashin iskar gas,” in ji ta.

Yadda farashin gas yake a wurin dillalai

A Jihar Kano, wani babban dillalin gas, Ultimate Gas yana siyar da iskar gas akan N960 duk kilo a cibiyarsa ta Sharada, don haka ana cika tukunya mai kilo 2 akan N1, 920, yayin da mai kilo 6 da 12 ake cika su akan N5,760 da N11,520.

Haka zalika, AA Rano wanda shi ma babban dillalin gas ne yana siyar da gas din akan N926 duk kilo daya.

A Ilorin, galibin gidajen mai na sayar da iskar gas tsakanin N950 zuwa N1,050 kan kowace kilo, yayin da sauran gidajen sayar da man ke sayar da shi tsakanin N1,100 zuwa N1,150 duk kilogiram.

A Abuja dai farashin kilogiram N1,100 ne a gidajen sayar da mai a ranar Laraba, kamar yadda masu lura da al’amuran suka ce sun saya ne a tsakanin N850 zuwa N900.

A Legas kuwa, ana sayar da shi kan Naira 950, a wasu tashoshin yayin da wasu kuma suke sayar da shi kan Naira 1,100.

A wata tashar mai da ke Ile Epo, daura da babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta, wakilinmu ya lura da dogayen layukan kwastomomi da ke sayen duk kilogiram daya a kan Naira 1,100.

‘A hakan ma an samu rangwame saboda tsoma baki da Tinubu ya yi’

Da yake zantawa da Aminiya, Shugaban kungiyar dillalan iskar gas ta Najeriya (NALPGAM), Oladapo Olatunbosun, wanda tun da farko ya yi korafin cewa iskar gas na iya kaiwa Naira 1,500 kan kowace kilogiram a watan Disamba, ya ce shiga tsakani da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya sa farashin bai wuce yadda ake tsammani ba.

Ya bayyana cewa da ba don tsoma baki da Tinubu ya yi ba, zuwa yanzu farashin gas din girki tuni ya haura Naira 1,500 duk kilogiram daya.