✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bam: Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan ya sha da kyar

Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan Amrullah Saleh, ya tsallake rijiya da baya a wani harin bam da aka kitsa a gefen hanya a Kabul babban birnin…

Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan Amrullah Saleh, ya tsallake rijiya da baya a wani harin bam da aka kitsa a gefen hanya a Kabul babban birnin kasar.

Kungiyar Taliban ta musanta zargin kai harin da ya zo a daidai lokacin da ake shirin zaman sulhu tsakaninta da gwamnatin Afghanistan a kasar Qatar.

“Makiya Afghanistan sun yi kokarin hallaka Saleh amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, Saleh ya tsira daga mummunan hari da aka kai masa”, inji kakakinsa, Razwan Murad.

Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa harin bam din din da aka kai da nufin hallaka Saleh ya raunata masu tsaronsa.

Harin na ranar Laraba ya kashe mutum 10 sannan ya raunata mutum 15 kamar yadda Ma’aikatar Cikin Gida ta bayyana.

“Wannan harin ba zai dakatar da mu daga yunkurinmu na kawo zaman lafiya a kasarmu ba”, a cewar Javid Faisal mai Magana da yawun jami’an tsaron kasar.

Saleh ya bayyana a wani bidiyo jim kadan bayan harin cewa ya samu dan kuna a fuskarsa da wani karamin rauni a hannunsa.

Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan Amrullah Saleh
Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan, Amrullah Saleh

Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mayakansu ba su da hannu a harin.

Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asiri na Shugaba Ashraf Ghani, ya sha kubuta daga irin wadannan hare-hare, ciki har da wanda ya rutsa da rayukan mutum 20.