✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Filato: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro

Ana zargin hukumomin tsaron da rashin aiki da bayanan da aka bayar kafin harin da kuma rashin hadin kai tsakaninsu

Majalisar Dattawa ta bukaci shugabannin hukumomin tsaro su bayyana a gabanta su tambayoyi kan kisan gilla da aka yi wa mutane 145 da Kirsimeti a Jihar Filato.

Yan bindiga sun yi wannan aika-aika ne kauyuka 23 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi inda suka jikkata daruruwan mutane suka lalata dukiyoyi daga ranar Asabar har zuwa safiyar Litinin, Kirsimeti.

Majalisar ta ce hare-haren da ’yan bindiga suka kai a tare a lokaci guda ya nuna akwai gazawa wajen samun bayanan sirri na tsaro.

Bayan kudirin da Sanata Diket Plang daga jihar ya gabatar a zaman majalisar na ranar Asabar, ta gayyaci daukacin shugabannin hukumomin tsaro su zo su yi bayani kan kashe-kashen a safiyar Litinin domin bai wa majalisar damar daukar mataki na gaba.

Wadanda aka gayyata su ne: Babban Hafsan tsaro, manyan hafsoshin sojin sama na kasa da na ruwa da shugaban hukumar DSS, mashawarcin shugaban kasa harkokin tsaro da shugaban hukumar leken asiri da shugaban ’yan sanda.

Shugabna Sanatocin Arewa, Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi), ya bayyana harin a matsayin wanda ba a taba gani ba.

Abdul Ningi ya ce binciken da gudanar a sa’o’i 72 a Filato inda suka gana da gwamnan jihar ya nuna maharan su kusan 400 sun kai hare-haren ne cikin tsari.

Ya ce ’yan bindigar sun ci karensu babu babbaka, yana mai zargin jami’an tsaron da rashin aiki da bayanan da aka bayar kafin a kai harin da kuma rashin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.

Gwamna Simon Lalong, ya yi watsi da ikirarin da sojoji suka yi na cewa yankin na da wahalar shiga kuma al’ummomin da aka kai harin sun yi nisa da inda sansanin sojoji.

Ya bayyana rashin jin dadinsa cewa duk da ayyukan soji daban-daban da suka hada da ‘Operation Safe Haven’ na wanzar da zaman lafiya a jihar, ana asarar rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba.