✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya kashe mutum 5 a Ogun

Ana zargin tukin ganganci ne ya haddasa hatsarin.

Akalla mutum biyar ne suka mutu yayin da biyu suka yi rauni a wani hatsarin mota da ya auku a kan titin Ota zuwa Idiroko a Jihar Ogun.

Aminiya ta gano cewa mutum biyar din sun mutu ne ranar Alhamis bayan faruwar hatsarin.

  1. Allah Ya yi wa Sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu rasuwa
  2. Matasa sun yi zanga-zanga a Fadar Sarkin Musulmi

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) a Jihar, Ahmed Umar, ya tabbatar da faruwar hatsarin a Abeokuta, inda ya ce lamarin ya faru a daren Alhamis da misalin karfe 11:45, tsakanin mota kirar Toyota Camry da wata babbar mota dauke da man diesel.

Malam Ahmed ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon tukin ganganci da direban Camry din ya yi, wanda a dalilin haka ya kasa rike motar.

“Abin da muke zargin ya haddasa hatsarin shi ne tukin ganganci da direban Camry ya yi har ya afkawa motar man dizel,” inji shi.

Ya kara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum bakwai, maza biyar mata biyu; kuma biyar daga ciki sun rasu.

Kwamandan na FRSC ya kuma ce an garzaya da wadanda suka yi raunin zuwa asibitin Cranft don ba su kulawa, wadanda suka mutu kuma an dauke su zuwa babban asibitin Otta.