✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi sanadiyyar ajalin mutum 2 a Jigawa

Mutum biyu da ke kan babur sun rasu sakamakon raunuka da suka samu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum biyu a wani hatsarin mota da ya faru a kan titin Hadeja zuwa Kano da ke Karamar Hukumar Ringim a Jihar.

ASP Shiisu Adam, wanda shi ne Kakakin Rundunar a jihar ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse, inda ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe.

  1. Jiragen yaki sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta
  2. Mutumin da ya fi kowa yawan iyalai a duniya ya kwanta dama

Ya ce, “Ranar 13 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 11 na safe hatsari ya faru tsakanin babur da mota a kan titin Hadeja zuwa Kano kusa da makarantar kwana ta Ringim.

“Lamarin ya ritsa da mota mai lambar DAL 87 AZ, da wani mai suna Mustapha Ibrahim daga unguwar Dakata daga Jihar Kano.

“Bayan mun isa wurin muka tarar da direban motar sun hadu da mai babur din, Auwalu Aminu wanda ya goyo abokinsa daga unguwar Tsigi.

“Sakamakon mummunan rauni da wanda suke tuka babur din suka samu sun rasu, bayan an kai su babban asibitin garin Ringim,” cewar kakakin ’yan sandan.

Idan ba a manta ba, ko a kwanakin baya Aminiya ta rawaito yadda mutum 18 suka rasu a wani hatsarin mota a kan titin Birnin Kudu zuwa Kano a Karamar Hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.

Hatsarin ya faru ne sakamakon gaba-da-gaba da ababen hawa biyu suka yi, wanda nan take wuta ta kama ta kone mutum 12, ragowar shida kuma suka rasu daga baya sakamakon raunukan da suka samu.