✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawa ’yan APC sun tsallake rijiya da baya a ranar zaɓe a Ibadan

Gwamna Makinde ya taya dukkan shugabannin kananan hukumomi 33 da kansilolinsu murnar lashe wannan zaɓe.

Zaɓen shugabannin Kananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar a Jihar Oyo a ranar Asabar da ta gabata ya ritsa da wasu ’yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar APC inda suka sha da kyar.

Lamarin ya auku ne a lokacin da ’yan Arewar suka zargi wasu magoya bayan Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar da karkatar da akwatunan zaɓe cike da kuri’u daga unguwanninsu zuwa wani wuri.

Alhaji Murtala Amadu Kofa, Shugaban ’Yan Arewa Magoya Bayan Jam’iyar APC a Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa ya ce “Mutanenmu sun tsallake rijiya da baya a hannun wasu magoya bayan PDP, waɗanda suka lakaɗa masu duka tare da korar su a kokarinsu na hana karkatar da wasu akwatunan zaɓe ɗauke da Iiuri’u a ciki zuwa wani wuri daban.

“Hakan ya auku ne bayan kammala zaɓe a ranar Asabar inda aka yi nufin ajiye akwatunan a wurin sirri zuwa wayewar garin Lahadi da za a kidaya Iiuri’un cikinsu.”

Murtala Amadu Kofa ya ce “Tun kafin a yi zaɓen aka fara ɓoye wasu akwatuna da aka keɓe wa rumfunan zaɓe na Unguwar Sabo mazaunin Hausawa a Ibadan.

“Mun miƙa kukanmu zuwa hedikwatar Karamar hukumar aka Iii sauraronmu.

“Maimakon haka ma aka fatattaki mutanenmu da duka inda wasu suka sha da Iiyar da raunuka a jikinsu.

“Amma shugabannin jam’iyarmu ta APC a Jihar Oyo masu son zama lafiya ne, sai suka nemi mu yi haIiuri domin guje wa ɓarkewar rikici a jihar tare da yi mana alIiawarin ɗaukar matakin shawo kan wannan matsala,” in ji shi.

Aminiya ta tuntuɓi tsohon kansilan mazaɓar Sasa kuma Mai ba Sanata Yunus Akintunde na Oyo ta Tsakiya Shawara kan Harkokin Ciki da Waje Alhaji Haruna Yaro wanda ya ce “Akwatuna 92 Hukumar Zaɓe ta Jihar Oyo (OYSIEC) ta keɓe domin kaɗa Iiuri’a ga mazauna Sasa da kewaye amma akwatuna 39 kawai aka kai a ranar zaɓen bayan ɓacewar sunayen.

“Alhaji Murtala Amadu Kofa Shugaban ‘Yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ibadan ta Arewa mutanenmu a rumfunan zaɓe.

“Wannan lamari ya ɓata wa mutanenmu rai kwarai da gaske musamman yadda wasu mutane suka yi amfani da madafun iko na Gwamnatin Jihar domin take haIiIiinmu,” in ji shi.

Wani Bahaushe da ke zaune a Unguwar Ojo a hanyar Bariki a Ibadan, Alhaji Muhammed ƊanIiasa ya ce “Muna da yawa da muke zaune tare da iyalinmu a wannan unguwa. Mun ki fita kaɗa kuri’a a wannan rana ce saboda mun san cewa an riga an kammala zaɓen.

“Kasancewa nau’in mutum 3 ne suka yi wannan zaɓe. Na farko su ne waɗanda aka raba masu kuɗi su kaɗa Iiuri’a.

“Na biyu kuma ’yan siyasa ne masu ra’ayin Jari-Hujja. Sai na uku su ne dangin waɗanda suka tsaya takara da abokansu.

“Saboda Alhaji Nasir Muhammed (SA) Shugaban ‘Yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar PDP a Unguwar Mokola Ibadan haka ban ga dalilin ɓata lokaci a cikin dogon layi ka zaɓi wanda kake so amma a mayar da Iiuri’arka ga mutanen da ba su cancanci yi wa jama’a jagoranci ba.”

Shi ma Yakubu Sakatare mazaunin Unguwar Oja-Oba a Ibadan cewa ya yi “A gaskiya mutanenmu ’yan Arewa mazauna wannan unguwa sun girmama doka da oda wajen rufe shaguna suka yi zamansu a gida domin bin umarnin mahukunta. Sai dai mafi yawa ba mu fito zaɓen ba.”

Shi kuwa jagoran ’yan Arewa magoya bayan Jam’iyyar PDP a Unguwar Mokola Ibadan, Alhaji Nasir Muhammed (SA) cewa ya yi “Mun gode wa Allah da Ya kai jam’iyyarmu ta lashe zaɓe a Iiananan hukumomi 33 na Jihar Oyo.

“Kuma a matsayinmu na ’yan Arewa mazauna wannan sashe muna yin aiki da shawarar magabata ne kamar Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello da Malam Aminu Kano da suka faɗi a wancan zamani cewa bai kamata ’yan Arewa da ke zaune a Kudu su riIia yin siyasa irin ta Arewacin Iiasa ba.

“Sun ce kamata ya yi mu shiga cikin siyasa irin wacce al’ummar da muke zaune tare da su suke yi.

“Hakan ne ya sa muka tsunduma cikin Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Oyo inda muke zaune.

“Kuma muna bayar da shawara ga mutanenmu su zo a yi wannan tafiya tare da su domin samun ci gabanmu a wannan sashe na kasa,” in ji shi.

Tun kafin a kammala zaɓen a ranar Asabar Jam’iyyar APC ta fara caccakar yadda aka gudanar da zaɓen.

Ta nemi Hukumar OYSIEC ta soke zaɓen baki ɗaya kuma ta tsayar da sabuwar ranar da za a sake sabon zaɓe a dalilan matsalolin rashin isar jami’an hukumar da kayan aiki a cikin lokaci a wasu rumfunan zaɓe da Iiarancin kayan aiki da rufe wasu rumfunan da aka yi ba tare da cikakken bayani ga masu ruwa-da-tsaki ba.

Da yake kare kansa a kan masu sukar gwamnatinsa Gwamna Seyi Makinde bayan kaɗa kuri’arsa a rumfar zaɓe ta kan hanyar Iwo a Ibadan, ya jinjina wa Hukumar OYSIEC kan irin rawar da ta taka wajen gudanar da zaɓen lami lafiya a faɗin jihar.

Ya ce ba a taɓa yin zaɓe mai tsafta kamar wannan a jihar ba.

Gwamna Makinde da jam’iyyarsa ta PDP sun taya dukkan shugabannin kananan hukumomi 33 da kansilolinsu murnar lashe wannan zaɓe.

Wasu bayanai da Aminiya ta samu daga mazauna wasu garuruwa a jihar sun nuna cewa an samu jinkirin fara zaɓen tare da ɓacewar sunayen jama’a a wasu rumfuna. Kuma ba a ga dogayen layukan mutane masu kaɗa kuri’a a rumfunan zaɓe ba.

Bayanan sun tabbatar da cewa ba a samu yawan hatsaniya da rikici ko kone- konen rumfunan zaɓe da kadarori a lokutan zaɓen ba.