Hisbah ta kama mai kyamis din da ke ‘lalata’ da mata a Kano | Aminiya

Hisbah ta kama mai kyamis din da ke ‘lalata’ da mata a Kano

    Sani Ibrahim Paki

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta tabbatar da kama wani mai sana’ar shagon sayar da magunguna (kyamis) da ake zargi da amfani da wani gida sabanin kyamis din wajen lalata da mata.

Dubun mutumin, mazaunin anguwar Sabuwar Gandu da ke birnin Kano ta cika ne ranar Juma’a lokacin da jami’an tsaron unguwar suka kama shi bayan ya shiga da wata budurwa gidan da nufin dubata a ciki.

A cewar Kakakin hukumar ta Hisbah, Lawan Ibrahim Fagge, ankarar da mazauna unguwar suka yi ne yasa suka yi kukan kura suka kama shi tare da damka shi ga hukumar domin a yi wa tufkar hanci.

Mazauna unguwar dai sun yi zargin cewa mutumin ya jima yana aikata ta’asar inda ya ware gidan wanda babu kowa a ciki yana kai mata da nufin zai duba su a ciki.

Tuni dai Babban Kwamandan hukumar, Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya umarci dakarun Hisbar su fadada bincike kan wanda ake zargin.

A nasa bangaren, mai kyamis din ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata tare da neman afuwar hukumar, yana mai alkawarin ba zai sake yi ba a nan gaba.