HOTUNA: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad na neman takarar dan majalisa | Aminiya

HOTUNA: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad na neman takarar dan majalisa

    Aliyu Jalal

Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmad, ya shiga jerin masu neman taraka a zaben 2023.

Bashir Ahmad, yana zawarcin kujerar dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu na Jihar Kano a zaben da ke kara matsowa.

Tuni fastocinsa suka fara yawo kuma ya riga ya gana da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, kan neman takarar tasa.

A yayin da yake ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki a yankin mazabar, ga wasu daga hotunan:

 

Bashir Ahmad yana gaisawa da jama’a a yayin da ya fito zagaye a mazabar da yake son wakilta a Majalisar Wakilai a 2023.

Tuni dai Bashir Ahmad ya sanar da Gwamna Ganduje game da aniyarsa ta wakiltar al’ummar Mazabar Gaya, Ajingi, Alabasu a Majalisar Wakilai.

Tuni aka fara ganin fastocinsa na neman kujear dan majalisa mai wakiltar Gaya, Ajingi da Albasu.

Hadimin shugaban kasar yana ganawa da sarakuna da malamai a yankin mazabar game da aniyarsa ta tsayawa takara

Hadimin na shugaban kasa zai yi takarar ne a karar inuwar jam’iyyar APC mai mulki.

Matasa sun yi ta gaisawa da su a lokacin da ya fito zagayen.

Sai kai-komo yake ta yi tsakanin al’ummar Gaya, Ajingi, Albasu domin samun goyon bayansu.

A nan shi ne yake daga wa jama’a hannu a lokacin zagayen nasa.